An Samu Karin Yan Ta'addan ISWAP sama da 20 da Suka Mika Wuya ga Sojoji
- Wasu ’yan uwa 24 na ’yan ta’addan kungiyar ISWAP da ta addabi sassan Najeriya sun mika wuya ga Sojojin Najeriya a Mafa ta Jihar Borno
- Haka kuma a wannan mako, sojojin sun kama wasu mutane da ake zargi da safarar makamai da taimaka wa ’yan ta’adda a Borno da Delta
- Sojoji sun ceto wata mata da aka sace a Kaduna, tare da kwato bindigu da shanu akalla 20 da aka sace a jihar Filato da ke Arewacin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Borno –Rundunar Sojin Najeriya ta ce wasu ’yan uwa 24 na ’yan ta’addan kungiyar ISWAP, sun mika wuya ga dakarunta a karamar hukumar Mafa ta Jihar Borno.
Rundunar ta bayyana cewa ce ’yan uwan ’yan ta’addan sun mika wuya ne da misalin karfe 4 na yammacin ranar Alhamis 20 ga watan Agusta, 2026 ga dakarun Bataliya ta 112 ta rundunar hadin gwiwa.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta kawo labarin cewa mutanen sun tsere daga sansanonin ’yan ta’addan da ke Gasuwa da Yaganari ne bayan barkewar fada tsakanin bangarorin da ke hamayya da juna a cikin kungiyar ta’addancin.
Sojoji sun yi samame a Najeriya
Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa rundunar ta ce an yi wa mutanen da suka mika wuya rajista tare da tattara bayanansu domin daukar matakin da ya dace.
A wani samame kuma, dakarun Bataliya ta 212 tare da hadin gwiwar kungiyar CJTF, sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da aikata laifuka a yankin Bewac.

Source: Original
An gudanar da samamen ne a kan hanyar Al-Ansar University da ke cikin Maiduguri, bisa bayanan sirrin da aka samu kan ayyukan da ake zargin na ’yan ta’adda ne.
Rundunar ta ce:
“Dakarun sun kama wani mutum dauke da kwandon harsashi da ke dauke da harsasai."
An kama dan ISWAP da makamai
Rahoton ya kuma ce dakarun Rundunar Leken Asirin Soji ta 25 tare da CJTF sun kama wani mutum da ake zargi da kai wa ’yan ISWAP kayayyaki da kuma yi musu leken asiri a Kekura, karamar hukumar Damboa ta Borno.
An kama wanda ake zargin a gidansa ne bayan bayanan sirri sun alakanta shi da kai kayan abinci da wayoyin hannu zuwa sansanonin ’yan ta’addan.
A Kaduna kuwa, rahoton ya ce dakarun Operation FANSAN YAMMA sun dakile yunkurin sace mutane a kauyen Jurawa da ke karamar hukumar Lere.
Rundunar ta bayyana cewa an ci gaba da bincike game yayin da ake ci gaba da kokari wajen magance matsalolin tsaron kasar nan.
Sojoji sun harbe dan ta'adda
A wani labarin, mun wallafa cewa dakarun sojojin Operation Fansan Yamma sun ceto wani mutum da ’yan ta’adda suka yi garkuwa da shi a jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya.
Jami'an sojojin sun kuma dakile wani hari da ’yan ta’adda suka kai a jihar Sokoto, inda suka kashe ɗaya daga cikin maharan a wani yunkuri na hana shi ci gaba da aikin ta'addanci.
A yayin samamen, sojojin sun kwato wayoyin hannu, kuɗi, katin ATM da katunan waya, kuma rundunar ta yi kira ga jama’a inda suka sha alwashin ci gaba da yaki da ta'addanci,
Asali: Legit.ng

