'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari, An Sace Matar Hakimi da Likita a Kaduna

'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari, An Sace Matar Hakimi da Likita a Kaduna

  • Masu garkuwa da mutane sun kashe wasu mazauna kauyen Abu biyu yayin da suke kokarin tserewa da likita da matar Hakimi da suka sace
  • Sojojin Operation Enduring Peace sun kaddamar da farmaki da aikin ceto domin kubutar da wadanda aka sace a karamar hukumar Sanga ta Kaduna
  • An gano matakin da jami'an sojin suka dauka a kokarin ceto matar da likitan da a yanzu haka ke tare da yan bindigar da suka kai harin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna –Dakarun Operation 'Enduring Peace' (OPEP) sun kaddamar da aikin ceto da farmaki bayan wasu masu garkuwa da mutane sun kaihari.

Rahotanni sun tabbatar da cewa 'yan bindigan sun sace wani likita da matar Hakimi a karamar hukumar Sanga ta Jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun sace matar sarki, sun hau TikTok sun nemi a aiko masu N20m

Yan bindiga sun kai mummunan hari jihar Kaduna
Wasu daga cikin jami'an tsaro a Najeriya Hoto: @NigeriaArmyInfo
Source: Facebook

Lamarin ya faru ne da misalin 7.40 na safe ranar Lahadi, 23 ga watan Agusta, 2026, a kauyen Abu da ke gundumar Ninzo, karamar hukumar Sanga.

Zagazola Makama ya wallafa shafin X cewa wata majiya daga bangaren tsaro ta ce dakarun da aka jibge a Raga sun mayar da martani kan rahoton sace Dakta Ezekiel Audu da matar Hakimin yankin.

An kai hari jihar Kaduna

Bayanai na farko sun nuna cewa masu garkuwar sun bude wa wasu mazauna yankin wuta bayan mutanen sun yi kokarin tunkararsu a lokacin da suke tsere wa da wadanda suka sace.

An ce harbin ya yi sanadin mutuwar mutanen yankin biyu yayin da jama'a suka rika gudun neman tsira da rayuwarsu daga harin.

An tafi neman garkuwa da mutane a Kaduna
Taswirar jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Bayan samun rahoton, dakarun sojin sun fara aikin ceto da farmaki bisa bayanan sirri da suka nuna yiwuwar masu garkuwar sun fake a wani wuri bayan sun tsere daga yankin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi awon gaba da basarake da wasu mutane

Dakarun sun nufi wurin da aka gano domin dakile masu laifin tare da kokarin kubutar da wadanda aka sace domin sada su da yanuwansu.

Halin da ake ciki bayan harin Kaduna

Rahotanni sun bayyana cewa har zuwa lokacin da aka fitar da rahoton harbin, sojojin ba su yi arangama da masu garkuwar ba.

Rundunar sojin ta ce tana ci gaba da kokarin gano inda aka boye wadanda aka sace domin kubutar da su tare da cafke wadanda suka aikata laifin.

Haka kuma, jami’an tsaro sun kara sanya ido a yankin yayin da aikin neman wadanda aka sace da farautar masu garkuwar ke ci gaba.

Yan bindiga sun kai wani hari Kaduna

A baya, kun samu labarin cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kashe jami’in tsaro na JTF a jihar Kaduna da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Rahotanni sun ce harin ya faru da misalin ƙarfe 11.00 na dare a Kyauta New Millennium City da ke ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna inda jamaa suka shiga kunci.

Jami'an tsaro na 'yan sa-kai sun bi sawun maharan wadanda suka zo suka aikata ta'asa kan mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba domin su girbi abin da suka shuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng