Musulmai Sun Dauki Mataki Mai Tsauri da Aka Gano Yan Bindiga na Shirin Kai Hari Masallatai
- DSS ta yi gargadi kan wani shirin kai hari wuraren ibada a Osun, lamarin da ya sa Kiristoci da Musulmi suka ɗauki matakan tsaro
- Kungiyar CAN ta umurci coci-coci su ƙarfafa tsaro tare da binciken baƙin da ke ziyartar wuraren ibada
- Ƙungiyar Musulmin Osun ta bi sahun CAN, inda ta buƙaci limamai su ƙara sa ido kan baƙi da kuma sanar da hukumomin tsaro duk wani motsi da ake zargi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Osun, Nigeria - Bayan Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) ta yi gargadi kan wani zargin shirin kai hari wuraren ibada a jihar Osun, Ƙungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) da al’ummar Musulmi sun ɗauki matakan hana yiwuwar kai hare-hare.
Lamarin ya biyo bayan wasu taruka daban-daban da DSS ta yi da shugabannin addinai a Osogbo a makon da ya gabata, inda aka ce ta shawarce su da su ɗauki matakan kariya daga yiwuwar hare-hare.

Source: Twitter
Vanguard ta ce gargadin ya zo ne bayan wani rahoton sirri da ke cewa ‘yan ta’adda na shirin yaɗa rashin tsaro zuwa kudancin ƙasar, musamman Kudu maso Yamma.
CAN ta ƙarfafa tsaron coci a Osun
A martaninta, kungiyar CAN ta jihar Osun ta ce ta ɗauki matakai domin ƙarfafa tsaro a kusa da coci-coci da kuma kare masu ibada bayan gargadin da DSS ta yi.
Shugaban CAN na jihar, Fasto John Adeleke, ya buƙaci coci-coci su haɗa kai da ƙungiyar wajen aiwatar da matakan.
Ya ce matakan sun haɗa da ƙarfafa sassan tsaron coci da kuma yin cikakken bincike kan sababbin fuskokin da ke ziyartar wuraren ibada.
Adeleke ya kuma buƙaci coci-coci su duba motocin da ke shiga harabar su sosai, sannan idan ya zama dole su binciki jakunkunan da ake shigowa da su cikin harabar coci.
Ya ce:
“Mun kuma ƙarfafa wa coci-coci gwiwa da su yi gaggawar sanar da jami’an tsaro idan suka lura da wata matsalar tsaro ko haɗari a yankunansu. Su hana yin tsayuwar dare, zuwa wuraren shakatawa da tafiye-tafiye ga mambobi.
Matakan da musulmi suka dauka
Haka kuma, Jami’in Hulɗa da Jama’a na al’ummar Musulmin Osun, Hameed Oyegbade, ya ce ƙungiyar ta shawarci manyan limamai da shugabannin masallatai su ƙara sa ido kan baƙin da ke zuwa masallatai domin yin salla.
“Ga manyan limaman sallolin Juma’a, mun buƙaci su ƙara taka-tsantsan tare da tabbatar da kasancewar jami’an tsaro yayin sallar Juma’a, da kuma tabbatar da cewa ba a ajiye motoci ko babura kusa da gine-ginen masallatai.
“Mun kuma ɗora wa limamai alhakin yin amfani da minbaransu wajen yaɗa saƙon taka-tsantsan a faɗin jihar, sanar da hukumomin tsaro duk wani motsi da ake zargi, sannan kada su yi kasadar bai wa baƙi mafaka ba tare da sun san su sosai ba,” in ji shi.

Source: Original
Abin da hukumar DSS ta hango
kun ji cewa hukumar DSS ta gargadi shugabannin Musulmi da Kirista a Osun kan zargin shirin ’yan ta’adda na kai hare-hare wuraren ibada da tarukan jama’a.
Rahotanni sun ce ana zargin shirin na daga cikin ƙoƙarin kawo cikas ga babban zaɓen 2027, ta hanyar haifar da rashin tsaro da fargaba a tsakanin al’umma.
Asali: Legit.ng

