Duk da Yana Uban Al'umma, Babban Sarki Ya Goyi bayan Tazarcen Tinubu

Duk da Yana Uban Al'umma, Babban Sarki Ya Goyi bayan Tazarcen Tinubu

  • Oba Rilwan Akiolu ya ce zai goyi bayan ƙoƙarin Shugaba Bola Tinubu na sake lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2027
  • Sarkin ya buƙaci ’yan siyasa su tabbatar da an gudanar da zaɓen 2027 cikin lumana, tare da guje wa matakan da za su kawo rashin zaman lafiya
  • Abdulaziz Yari ya ce kwamitin yaƙin neman zaɓen APC ya nemi albarka da shawarwarin Oba Akiolu, tare da yin kira ga ’yan Najeriya su sake zaɓar Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Legas - Oba na Legas, Rilwan Akiolu, ya bayyana goyon bayansa ga Shugaba Bola Tinubu domin ya sake yin wa’adin mulki na biyu.

Sarkin na Legas ya bayyana cewa babu gurbi a Aso Rock nan da shekaru huɗu ko biyar masu zuwa nan gaba.

Akiolu ya goyi bayan Tinubu
Abdulaziz Yari na jawabi a gaban Oba na Legas Hoto: Al'mansoor Gusau
Source: Facebook

Sarkin ya bayyana hakan ne lokacin da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC, ƙarƙashin jagorancin Abdulaziz Yari, ya kai masa ziyarar ban girma a fadarsa da ke Legas ranar Litinin, 14 ga watan Satumban 2026.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya bayar da shawara kan mutanen da za a zaba a 2027

Oba Akiolu ya yi magana kan zaɓen 2027

Oba Akiolu ya ce, “A cikin shekaru huɗu ko biyar masu zuwa, babu gurbin zama a Aso Rock.”

Sarkin ya kuma buƙaci ’yan siyasa su tabbatar da cewa babban zaɓen 2027 ya kasance cikin lumana kuma an gudanar da shi ta hanyar da za ta amfani ’yan Najeriya.

Ya shawarci mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen APC da su kasance masu gaskiya a mu’amalarsu, tare da guje wa duk wani mataki da zai iya kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin ƙasa.

Ya gargadi ’yan siyasa kan neman nasara ta kowace hanya

Oba Akiolu ya kuma ja kunnen ’yan siyasa kan amfani da tsarin tunanin Machiavelli na cewa “manufa ce ke tabbatar da halacci” wajen neman samun nasarar zaɓe.

Ya nuna cewa bai kamata ’yan siyasa su bi duk wata hanya ba kawai saboda suna son cimma nasarar zaɓe.

Yari ya nemi albarka da addu’ar Oba Akiolu

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Omokri ya gano 'sirrin' da zai yi tasiri kan Shugaba Tinubu

Tun da farko, Abdulaziz Yari ya ce tawagar ta ziyarci Oba Akiolu ne domin neman albarkarsa, addu’o’insa da shawarwarinsa gabanin fara ayyukan yaƙin neman zaɓen kwamitin a faɗin ƙasar.

Sanata Abdulaziz Yari ya ce kafin zuwa Legas, kwamitin ya fara ziyartar fadar Sarkin musulmi da ke birnin Sokoto.

Ya yi kira ga ’yan Najeriya da su ci gaba da mara wa Tinubu baya, yana cewa kwamitin ya yi imanin cewa shugaban ya cancanci sake samun wa’adin mulki domin ya kammala ayyukan da ya fara.

APC ta bayyana dalilan goyon bayan Tinubu

Yari ya ambaci ƙoƙarin gwamnatin Tinubu na magance matsalolin tattalin arziki, rashin tsaro da kuma bunƙasa ababen more rayuwa a matsayin wasu daga cikin dalilan goyon bayan sake zaɓen shugaban.

Ya amince cewa ’yan Najeriya na fuskantar matsin tattalin arziki, amma ya ce wasu alamu na nuna cewa tattalin arzikin na samun sauƙi, musamman wajen samun kuɗaɗe da ƙoƙarin da ake yi na daidaita tattalin arzikin ƙasar.

Game da tsaro, tsohon gwamnan Zamfara ya ce Tinubu na ci gaba da tallafa wa sojoji da ’yan sanda ta hanyar samar musu da kayan aiki.

Kara karanta wannan

Kurunkus: Tinubu, Atiku da Peter Obi sun bayyana hanyar da suka samu dukiyoyinsu

Oba na Legas ya goyi bayan Tinubu
Oba na Legas, Rilwan Akiolu na gabatar da jawabi Hoto: Al'mansoor Gusau
Source: Facebook

Dalibai sun goyi bayan Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa daliban manyan makarantun gaba da sakandare daga jihohin Arewa 19 da Babban Birnin Tarayya Abuja sun bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Sun yi alƙawarin ƙara wayar da kan ɗalibai da matasa kan shirye-shiryen gwamnatin tarayya gabanin zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng