Shugaba Tinubu Ya Tura Tawagar Gwamnoni Gidan Sheikh Jingir a Jos
- Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin siyasa, Ibrahim Kabir Masari, ya kasance cikin tawagar da ta kai ta’aziyyar Bola Tinubu ga Sheikh Sani Yahaya Jingir
- Tawagar ta ziyarci Sheikh Sani Yahaya Jingir a gidansa da ke Jos, babban birnin jihar Plateau, bayan rasuwar Hafiz Bala Yusuf, wanda aka fi sani da Ma’aji
- Tawagar ta miƙa saƙon ta’aziyyar Tinubu ga Sheikh Yahaya Jingir, iyalan marigayin da kuma al’ummar Musulmi tare da yi masa addu’ar samun rahamar Allah
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Ibrahim Kabir Masari, Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin siyasa da sauran al’amura, ya kasance cikin wata babbar tawagar gwamnatin tarayya da ta kai saƙon ta’aziyyar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ga Sheikh Sani Yahaya Jingir.
Tawagar ta ziyarci Sheikh Yahaya Jingir a gidansa da ke Jos, jihar Plateau, domin miƙa masa ta’aziyyar Shugaban Ƙasa bayan rasuwar Hafiz Bala Yusuf, wanda aka fi sani da Ma’aji.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanai game da ziyarar ne a wani sako da aka wallafa a shafin Facebook na Ibrahim Kabir Masari.
Buni ya jagoranci tawagar Tinubu
Rahotanni sun nuna cewa Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ne ya jagoranci tawagar da ta kai ziyarar ta’aziyyar.
Sauran mambobin tawagar sun haɗa da Gwamnan Kaduna, Uba Sani, Ibrahim Kabir Masari da Ministan Gidaje da Raya Birane, Dr Muttaka Rabe Darma.
Sun miƙa saƙon ta’aziyyar Shugaba Tinubu ga Sheikh Sani Yahaya Jingir, iyalan marigayin da kuma al’ummar Musulmi baki ɗaya.
An yi wa marigayin addu’a
Mambobin tawagar sun kuma yi ta’aziyya tare da jinjina wa Hafiz Bala Yusuf saboda gudunmawar da ya bayar wajen karatun addinin Musulunci da kuma raya a al’ummar Musulmi.
An gudanar da addu’o’i domin Allah Ya jiƙan marigayin, Ya gafarta masa kura-kuransa tare da ba shi Aljannatul Firdaus.
An kuma roƙi Allah Ya bai wa iyalansa, abokan hulɗarsa, ɗalibansa da sauran al’ummar Musulmi haƙuri da ƙarfin zuciya wajen jure wannan babban rashi.

Kara karanta wannan
Tinubu na ta samun goyon baya a Arewa, manyan malaman jami'o'i 600 sun bayyana matsayarsu

Source: Facebook
Dalilin ziyarar ta’aziyyar
Tawagar ta ce ziyarar ta nuna irin muhimmancin da gwamnatin Tinubu ke bai wa shawarwari da gudunmawar malaman addinin Musulunci da shugabannin addinai wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.
Haka kuma an bayyana muhimmancin rawar da malaman addini ke takawa wajen ƙarfafa fahimtar juna, zaman lafiya da haɗin kan al’umma.
Maganar Zulum kan Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan Borno, Babagana Zulum, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su ƙara haƙuri da ƙoƙarin gwamnatin tarayya na shawo kan matsalolin tsaro, talauci da sauran ƙalubalen ƙasa.
Zulum ya bayyana hakan ne a Kaduna bayan wata ganawa da shugabannin malamai mata na na Arewa da malaman addinin Musulunci, inda ya nemi agoyi bayan Tinubu.
Gwamnan ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin ƙarfafa haɗin kan Najeriya da kuma tabbatar da zaman lafiya tsakanin Arewa da Kudancin ƙasar.
Asali: Legit.ng
