Dangote Ya Sauya Kudin Fetur yayin da ake Magana kan Maido Tallafin Mai

Dangote Ya Sauya Kudin Fetur yayin da ake Magana kan Maido Tallafin Mai

  • Matatar Dangote ta kara farashin litar fetur daga N1,165 zuwa N1,185, bayan karin N20 da za a fara aiwatarwa daga tsakar daren ranar 21 ga Agusta, 2026
  • Karin farashin ya zo ne yayin da farashin danyen mai na Brent ya haura dala 93, sakamakon fargabar katsewar samar da mai da rikicin Amurka da Iran ya haddasa
  • Sabon farashin na Dangote ya kasance kasa da wasu manyan rumbunan ajiyar mai a Legas, yayin da man fetur ke sayuwa kan N1,190 zuwa N1,200

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar LagosMatatar Dangote ta kara farashin man fetur da N20 kan kowace lita, inda sabon farashin ya tashi daga N1,165 zuwa N1,185 kan kowace lita.

Sabon farashin zai fara aiki daga tsakar daren ranar Juma'a, 21 ga watan Agustan 2026, kamar yadda wasu rahotanni suka nuna.

Kara karanta wannan

Abin kunya: An kama matashin da ya shiga gida satar ɗan kamfan matar aure

Aliko Dangote da matatar man shi
Alhaji Aliko Dangote da matatar shi a gefen dama. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa karin farashin na zuwa ne a daidai lokacin da farashin danyen mai a kasuwar duniya ke ci gaba da hauhawa, sakamakon rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran.

Danyen mai ya haura dala 93

Rahoton Oilprice.com ya nuna cewa farashin danyen mai na Brent, wanda ake amfani da shi a matsayin ma'aunin farashin mai a kasuwannin duniya, ya karu da 1.95% zuwa $93.48 kan kowace ganga.

Haka kuma, farashin danyen mai na Amurka, wato WTI, ya karu da kusan 2% zuwa $86.12 kan kowace ganga.

Hakan ya sa Brent ya kai matsayi mafi girma cikin kusan makonni uku, yayin da fatan samun tattaunawa tsakanin Amurka da Iran ke kara raguwa.

Rahotanni sun nuna cewa farashin mai ya ci gaba da hawa na kwanaki biyar a jere, musamman bayan shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da abin da ya kira mafi tsananin matakin matsin tattalin arziki da Amurka ta taba dauka kan wata kasa.

Kara karanta wannan

An kama makudan kudaden kasashen waje a Kano, EFCC ta shiga bincike

Me sabon farashin ke nufi?

Kafin sabon sauyin, wasu manyan rumbunan ajiyar man fetur da ke Legas sun riga sun sayar da mai a kan farashi mafi tsada.

A Integrated Oil and Gas, African Terminals da NIPCO, ana sayar da litar man fetur kan N1,200, yayin da Pinnacle Oil and Gas ke sayar da shi kan N1,190.

Wani sashe na matatar Dangote
Matatar Dangote da ke jihar Legas. Hoto: Dangote Industries
Source: Getty Images

Sabon farashin Dangote na N1,185 ya kasance N15 kasa da farashin N1,200 da ake samu a wasu daga cikin rumbunan ajiyar man fetur uku.

Tinubu ya soki Atiku kan mai

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce alƙawarin Atiku Abubakar na dawo da tallafin man fetur ya nuna rashin fahimtar yadda shugabanci da tattalin arziki ke gudana.

Tinubu ya bayyana haka ne yayin da yake mayar da martani kan kalaman Atiku, wanda ya ce zai dawo da tallafin tare da bincikar yadda aka yi amfani da kudin da aka samu bayan cire shi.

Shugaban kasar ya ce kafin gwamnatinsa ta cire tallafin, jihohi da dama na fuskantar matsalar biyan albashin ma'aikata da fansho, yana mai cewa sauyin tsarin ya inganta kudin shiga na jihohi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng