'Trump na Goyon bayan Shirin Atiku na Dawo da Tallafin Man Fetur'
- Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ce Shugaban Amurka Donald Trump na goyon bayan shirinsa na dawo da tallafin man fetur
- Atiku ya ce manufarsa za ta mayar da kuɗi cikin aljihun ‘yan Najeriya ta hanyar tallafa wa samar da man fetur da tace shi a cikin ƙasa
- Ya bayyana hakan ne ranar Lahadi a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Phrank Shaibu, ya fitar, yayin da yake ci gaba da sukar manufofin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa Shugaban Amurka Donald Trump na goyon bayan shirinsa na dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban Najeriya a 2027.
Atiku ya sha alwashin dawo da tallafin man fetur, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen rage nauyin tsadar rayuwa da ke addabar ‘yan Najeriya.

Source: Facebook
PM News ta wallafa cewa mai magana da yawun Atiku Abubakar, Phrank Shaibu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Shirin Atiku na dawo da tallafi
Atiku ya ce shirin tallafin samar da man fetur da yake gabatarwa zai mayar da hankali ne kan tallafa wa abubuwan da Najeriya ke samarwa da tacewa a cikin gida.
Ya ce za a ƙara yawan man da ake samarwa, a sanya ido kan farashinsa, sannan a tabbatar da cewa ‘yan Najeriya sun amfana da matakin a gidajen mai.
“Wannan ne dalilin da ya sa tallafin samar da man fetur nawa ya shafi mayar da kuɗi cikin aljihun mutane.
"A tallafa wa abin da muke samarwa da tacewa a nan, a ƙara yawan abin da ake samarwa, a sanya ido kan farashi, sannan a tabbatar da cewa ‘yan Najeriya sun ji amfanin hakan a gidajen mai,”
In ji Atiku.
Alakar shirin da matakan Amurka
Atiku ya yi nuni da matsayin Ƙungiyar Masu Kamfanonin Tace Man Fetur ta Najeriya, wadda ke goyon bayan ƙara tallafa wa samar da man fetur a cikin gida.
Ya kuma ce matakan da Amurka ke ɗauka wajen ƙarfafa samar da makamashi da tace man fetur sun nuna muhimmancin tallafa wa samar da makamashi mai muhimmanci ga ƙasa.
Daily Post ta wallafa cewa ya ce:
“Ƙungiyar masu kamfanonin tace man fetur ta Najeriya na cewa a tallafa wa samar da kayayyaki a cikin gida. Amurka ta fahimci muhimmancin tallafa wa dabarun samar da makamashi,”

Source: Getty Images
Atiku ya zargi Bola Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya zargi Shugaba Bola Tinubu da ruguza tattalin arzikin ‘yan Najeriya.
Ya ce cire tallafin man fetur ya haifar da tashin farashin man fetur, sufuri da abinci, lamarin da ya ƙara wa ‘yan Najeriya wahalar rayuwa.
Atiku ya ce gwamnatin Tinubu na adawa da shirin tallafin samar da man fetur da zai rage wannan nauyi, duk da cewa hakan zai kawo sauki a kasar.
Asali: Legit.ng
