Dangote Ya Fara Raba Man Fetur Kyauta a Najeriya, Ya Fara da Jihohi 6 da Abuja

Dangote Ya Fara Raba Man Fetur Kyauta a Najeriya, Ya Fara da Jihohi 6 da Abuja

  • Matatar Dangote ta fara kai fetur kyauta zuwa jihohi shida da Abuja ga masu sayen lita 250,000 ko fiye ba tare da karin kudin sufuri ba
  • Kamfanin ya ci gaba da sayar da fetur kan Naira 1,075 kowace lita tare da ba kwastomomi damar biyan bashi na kwanaki 10
  • Masu kasuwancin mai sun ce matakin na iya kara rage farashin fetur tare da inganta wadatar mai a gidajen mai fadin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Legas - Matatar man Dangote ta fara kai fetur kyauta zuwa wasu jihohi shida da Babban Birnin Tarayya (FCT), Abuja.

Wannan na zuwa ne yayin da matatar Dangote ta ci gaba da sayar da fetur a farashin Naira 1,075 kan kowace lita ga abokan huldarta.

Matatar Dangote ta fara raba fetur kyauta a Najeriya
Alhaji Aliko Dangote (hagu), motocin dakon mai a gidan man Dangote (dama). Hoto: Getty Images
Source: UGC

Dangote ya fara raba fetur kyauta

Kara karanta wannan

Dangote ya zabi kasar da zai kafa sabuwar matatar mai a Afrika

Kamfanin ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Laraba.

A cewar matatar, shirin kai fetur ba tare da karin kudin sufuri ba ya shafi jihohin Legas, Ogun, Rivers, Kaduna, Delta da kuma Abuja.

Sai dai kamfanin ya bayyana cewa wannan dama ta shafi kwastomomin da za su sayi akalla lita 250,000 na fetur.

Baya ga kai fetur kyauta, matatar ta ce masu sayen da suka cancanta za su samu damar biyan kudin mai cikin kwanaki 10 bayan an kai musu kaya.

Sabon matakin ya zo ne bayan ganawar da matatar ta yi da masu ruwa da tsaki a bangaren kasuwancin man fetur domin tattauna batun farashin da ya dace da halin kasuwa.

Matatar Dangote ta rage farashin fetur

Bayan taron, masu ruwa da tsakin sun nuna goyon bayansu ga karin rage farashin fetur domin saukakawa masu amfani.

Matatar ta bukaci 'yan kasuwa da masu sayen mai da yawa su tuntubi sashen kai kaya na kamfanin domin samun cikakken bayani kan yadda za su shiga shirin.

Kara karanta wannan

Sauki zai samu: Dangote da wasu manyan dillalai sun rage farashin litar fetur

A kwanakin baya, Legit Hausa ta ruwaito cewa matatar ta rage farashin fetur a matata karo na hudu, inda ta daidaita shi zuwa Naira 1,075 kan kowace lita.

Shugaban Kungiyar Masu Kasuwancin Mai Masu Zaman Kansu (IPMAN), Abubakar Maigandi, ya bayyana cewa farashin fetur a gidajen mai ya ragu da Naira 125 kan kowace lita cikin makonni uku da suka gabata.

A cewarsa, farashin fetur yanzu yana tsakanin Naira 1,155 da Naira 1,299 kan kowace lita, gwargwadon yanki da kuma mai sayarwa.

Dangote ya bukaci 'yan kasuwa da su gaggauta cin gajiyar shirin sayen fetur a kawo masu kyauta.
Alhaji Aliko Dangote, attajirin Afrika da ke shirin gina matatar mai a Kenya. Hoto: Tom Saater/Bloomberg via Getty Images
Source: Getty Images

Kiran Dangote ga 'yan kasuwa

Haka kuma, matatar ta bude sayar da fetur kai tsaye ga dukkan masu kasuwanci da ke da lasisi, inda ta kawo karshen tsohon tsarin sayarwa ta hannun wasu kungiyoyi.

Dangote Group ya bukaci masu gidajen mai da dillalan fetur su yi rajista cikin gaggawa domin cin gajiyar wannan shiri.

Masana na ganin wannan mataki zai kara tabbatar da wadatar fetur tare da iya janyo karin saukin farashi a gidajen mai idan yanayin kasuwa ya ci gaba da kasancewa haka.

Dangote zai kafa sabuwar matatar mai

A wani labari, mun ruwaito cewa, Aliko Dangote ya zaɓi tsibirin Lamu da ke gaɓar tekun Kenya a matsayin wurin da za a gina sabuwar masana'antar mai ta Gabashin Afirka.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa mai ya sauka a duniya amma Dangote bai karya kudin fetur ba

Babban jami'in kamfanin Dangote ya shaida cewa ginin zai ɗauki watanni 30 kuma masana'antar za ta iya sarrafa ganga 700,000 a rana.

Rahotanni sun bayyana cewa Dangote ya gayyaci gwamnatin kasar Tanzania ta sanya hannun jari a aikin matatar da zai a yankin Lamu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com