‘Ku Fara Kare Kanku’: Dan Majalisar Amurka Ya Fada ya 'Yan Najeriya Gaskiya

‘Ku Fara Kare Kanku’: Dan Majalisar Amurka Ya Fada ya 'Yan Najeriya Gaskiya

  • Wani dan majalisar wakilan Amurka, Chris Smith, ya zargi gwamnatin Najeriya da gazawa wajen kare 'yan kasarta
  • Harin da aka kai ya rutsa da wasu mazauna Jwak Maitumbi da Bin-Per a Mangu, inda aka kashe mutane da dama
  • Smith ya bukaci gwamnatin Najeriya ta dauki matakin gaggawa, yayin da ya ce Amurka na bukatar a kare al'ummomin Kirista

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jos, Plateau - Wani dan majalisar wakila daga kasar Amurka, Chris Smith, ya zargi gwamnatin Najeriya da gazawa wajen kare 'yan kasar da kuma hukunta wadanda ke da hannu a hare-hare a Plateau.

An kashe wasu mazauna Jwak Maitumbi, wadanda ake zargin Fulani ne, a ranar 16 ga watan Agusta a karamar hukumar Mangu a Plateau.

Dan majalisar Amurka ya shawarci yan Najeriya
Dan majalisar wakilan Amurka, Chris Smith da Bola Tinubu. Hoto: Christopher Smith, Bayo Onanuga.
Source: Facebook

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Smith ya bukaci gwamnatin Najeriya ta dauki matakin gaggawa domin kare al'ummomin Kirista tare da tabbatar da an masu kai hare-hare, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Kotun Amurka ta dauki mataki kan neman sakin takardun zargin Tinubu

Hare-haren da aka kai a Plateau

Kasa da sa'o'i 48 bayan haka, wasu da ake zargin mayakan Fulani ne sun kai hari kauyen Bin-Per da ke yankin Kombun a Mangu, inda suka kashe akalla mutane 23, ciki har da mata da yara.

Lamarin ya bayyana a matsayin ramuwar gayya bayan harin farko da aka kai a Jwak Maitumbi.

A ranar Alhamis, dakarun Operation Enduring Peace sun dakile wani yunkurin kai hari kauyen Manja da ke karamar hukumar Mangu, bayan sun samu bayanan sirri kan wasu makiyaya dauke da makamai da ke tafiya da shanu a yankin.

Rahotanni sun ce wadanda ake zargin sun lalata gonaki tare da kokarin kai hari ga al'ummar yankin.

Ya ce:

“Duk da musanta lamarin da wasu jami'an gwamnatin Najeriya ke yi, ana ci gaba da kashe Kiristoci yayin da jami'an Najeriya suka kasa samar da isasshen tsaro ko hukunta wadanda suka aikata laifukan.
“Ya isa haka. Dole ne gwamnatin Najeriya ta cika babban nauyin da ke kanta na kare 'yan kasarta.”

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya fadi makamin Najeriya da 'yan bindiga ke jin bala'in tsoro

An kashe mutane a Plateau
Taswirar jihar Plateau da ke Arewacin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Bukatar dan majalisar Amurka ga Najeriya

Sanarwar ta ce Smith ya yi wannan magana tare da Frank Garcia, mataimakin ministan harkokin wajen Amurka mai kula da harkokin Afirka.

Garcia ya bukaci gwamnatin Najeriya ta cika alkawurran da ta dauka na kare al'ummomin Kirista da kuma tabbatar da an hukunta wadanda ke da hannu wajen tashe-tashen hankula.

Smith ya ce sakon da Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar kwanan nan ya nuna bukatar daukar matakan zahiri, ba wai karin alkawura kadai ba, yayin da tashin hankalin ke ci gaba da lalata rayuwar al'ummomin da ke cikin hadari.

Ya kuma ce maimakon gwamnatin Najeriya ta kashe miliyoyin daloli wajen kokarin inganta matsayinta a Washington, ya kamata ta karkatar da kudaden wajen kare 'yan kasa da magance matsalar tsaro, cewar Punch.

Smith ya ce gwamnatin Najeriya na kashe dala miliyan 9 wajen kokarin inganta matsayinta a Washington, inda ya bukaci a mayar da kudaden wajen tabbatar da tsaron al'umma.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun afka kan masu sallar Juma'a, sun saci adadin mutane mai yawa

CPC: Dan majalisar Amurka ya yi batun Najeriya

An ji cewa dan majalisar dokokin Amurka ya jaddada cewa bai kamata kasar ta cire Najeriya daga ƙasashen da ake zargi da take ’yancin addini ba.

Riley Moore ya ce karuwar kashe Kiristoci a yankin Arewa ta Tsakiya ya nuna akwai buƙatar ci gaba da matsa wa Najeriya lamba.

Ya yi wannan magana ne bayan farmakin da aka kai kwanan nan a jihar Filato, wanda ya yi ajalin mutane fiye da 20.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.