'Yan Bindiga Sun Afka kan Masu Sallar Juma'a, Sun Saci Adadin Mutane Mai Yawa

'Yan Bindiga Sun Afka kan Masu Sallar Juma'a, Sun Saci Adadin Mutane Mai Yawa

  • Rundunar 'yan sandan jihar Niger ta tabbatar da sace wasu masallata da ake zargin 'yan bindiga ne suka yi a karamar hukumar Borgu
  • An ce lamarin ya faru ne bayan kammala sallar Juma'a, inda maharan suka sace mutane daga wasu kauyuka da ke yankin
  • 'Yan sanda sun ce an tura jami'an tsaro domin ceto wadanda aka sace, sai dai lalacewar hanyoyi da rugujewar gada na kawo cikas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Niger – Rundunar 'yan sandan jihar Niger ta tabbatar da sace wasu Musulmi da ba a tantance adadinsu ba bayan kammala sallar Juma'a a wasu al'ummomin karamar hukumar Borgu.

An ce wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka kai harin, inda suka yi awon gaba da mutanen daga kauyukan Gidan Zana, Masaka, Sabon Gida da sauran kauyukan da ke makwabtaka da yankin.

Kara karanta wannan

Sojoji sun bi sawun yan bindiga da aka raunata, an kama mutum 2 da ke jinya a Adamawa

Wasu 'yan bindiga a Najeriya
Taron wasu 'yan bindiga masu kai hare-hare. Hoto: Zagazola Makama
Source: Twitter

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa lamarin ya faru ne ranar Juma'a, jim kadan bayan masallatan sun kammala sallar Juma'a a babban masallacin garin Dekara.

Yadda aka sace masallata a Neja

Rahotanni daga majiyoyin tsaro da wasu shaidun gani da ido sun nuna cewa maharan dauke da makamai sun mamaye yankin tare da yin awon gaba da wasu daga cikin mutanen.

Daga cikin wadanda aka ce an sace akwai mahaifin Hakimin garin Dekara, wanda aka bayyana cewa yana da shekaru 90 a duniya.

Leadership ta wallafa cewa kawo yanzu hukumomi ba su bayyana adadin mutanen da aka sace ba, yayin da ake ci gaba da tattara bayanai kan lamarin.

Harin ya kara tayar da hankalin mazauna wasu yankuna a Borgu, musamman al'ummomin da ke yankunan karkara wadanda ake ganin suna fuskantar barazanar hare-hare da sace-sace.

'Yan sanda sun fara aikin ceto

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Niger, SP Wasiu Abiodun, ya ce hukumomin tsaro sun tura jami'ansu domin fara aikin ceto wadanda aka sace.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sama da 100 sun tafka ta'asa yayin wani hari a Katsina

SP Abiodun ya ce kawo lokacin da yake magana, ba a samu rahoton mutuwar wani mutum dangane da harin ba.

Ya bayyana cewa jami'an tsaro na ci gaba da kokarin gano inda maharan suka nufa tare da cafke wadanda ke da hannu a sace mutanen.

Taswirar jihar Neja
Taswirar jihar Neja a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Kakakin 'yan sandan ya kuma ce an kara zafafa bincike da sintiri a yankunan da ake zaton maharan za su iya bi domin tserewa.

An kama DSS na bogi

A wani labarin kuma, mun ruwaito cewa Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta kama wani mutum mai suna Moferewa Maiye bisa zargin yin shigar jami'in hukumar.

An ce jami'an DSS sun bi sawunsa tare da cafke shi a maboyarsa da ke kusa da kwanar NITEL, a titin Adetokunbo Ademola da ke Wuse II a Abuja.

A lokacin da aka kama shi, rahotanni sun ce Maiye na sanye da kayan aikin DSS kuma yana dauke da bindiga ta bogi, yayin da ake zargin yana amfani da kayan hukuma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng