'Yan Bindiga Sun Kira Ruwa, Gwamnatin Sokoto Ta Dauki Gagarumin Matakin Murkushe Su
- Gwamnatin Sokoto ta ce ta ayyana yaƙi da ’yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka bayan wani mummunan hari da ya kashe mutane a Kebbe
- Gwamnatin jihar ta ware N9m ga iyalan mutane takwas da aka kashe da kuma mutum huɗu da suka jikkata domin rage musu radadin bala’in
- Kwamishina Jabir Sani Maihulla ya ce gwamnatin Ahmad Aliyu za ta ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro da kayan aiki da sauran abubuwan da suke buƙata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Sokoto - Gwamnatin jihar Sokoto ta ayyana “yaƙi na bai ɗaya” kan ’yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka da take zargi da haddasa ƙaruwar rashin tsaro a yankunan da ke cikin haɗari.
Matakin ya biyo bayan wani mummunan hari da aka kai a ƙaramar hukumar Kebbe, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane tare da jikkata wasu.

Source: Facebook
Gwamnatin jihar ta kuma bayar da tallafin kuɗi na N9m ga iyalan waɗanda suka mutu da kuma waɗanda suka tsira da raunuka domin rage musu tasirin wannan mummunan lamari, cewar rahoton jaridar Vanguard.
Tawaga ta ziyarci iyalan waɗanda abin ya shafa
A ranar Asabar, 5 ga watan Satumban 2026 wata babbar tawaga da Kwamishinan Harkokin Addini, Farfesa Jabir Sani Maihulla, ya jagoranta ta ziyarci yankunan da lamarin ya shafa.
Tawagar ta je ne bisa umarnin Gwamna Ahmad Aliyu Sokoto domin jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa ’yan uwansu, ta'azantar da waɗanda suka tsira tare da kai musu tallafin kuɗi da kayan abinci.
A cewar wata sanarwa daga Ofishin Sakataren ƙaramar hukumar Kebbe, matakin ya nuna ƙudurin gwamnatin jihar na cewa ba za ta yi watsi da al’ummomin da hare-haren ta’addanci da miyagun laifuka suka shafa ba.
Iyalan mamatan sun samu N8m
A cikin tallafin gaggawa, gwamnatin jihar ta bai wa iyalan mutane takwas da aka kashe N8m, inda kowace iyali ta samu N1m tare da buhunan kayan abinci guda biyar.
Haka kuma, mutane huɗu da suka jikkata sun samu N1m gaba ɗaya, wato N250,000 kowannensu.
Baya ga kuɗin, kowane ɗaya daga cikin waɗanda suka jikkata ya samu buhunan shinkafa, gero da masara guda uku kowanne.
Gwamna ya yi alƙawarin ƙara yaƙi da ’yan ta’adda
Da yake magana da iyalan mamatan da mazauna yankin, Maihulla ya bayyana damuwa da kisan, yana mai cewa harin ya jefa iyalai da al’ummar Kebbe cikin babban baƙin ciki.
Kwamishinan ya ce Gwamna Ahmad Aliyu ya ƙuduri aniyar ƙara ƙarfafa matakan da jihar ke ɗauka domin magance matsalar tsaro.
Ya ce gwamnati za ta ci gaba da amfani da dukkan albarkatun da take da su, ciki har da kuɗi da kayan aiki, wajen tallafa wa jami’an tsaro da ke gudanar da ayyuka a yankunan da lamarin ya shafa.
“Gwamnan yana yin duk abin da zai iya domin magance ƙalubalen tsaro, ciki har da samar da motocin aiki, kayan aiki da sauran taimakon da jami’an tsaro ke buƙata,” in ji Maihulla.

Source: Original
'Yan bindiga sun kashe mutane a Sokoto
A wani labarin kuma, kun ji cewa - ’Yan bindiga dauke da makamai sun kai hari ƙauyen Girkau da ke ƙaramar hukumar Kebbe a jihar Sokoto.
'Yan bindigan sun kashe aƙalla mutane biyar tare da jikkata wasu uku a yayin mummunan harin da suka kai a kauyen.
Asali: Legit.ng


