'Ya Ci Mana Mutunci': Jigon PDP Ya Caccaki Farfesa Pantami kan Siyasa
- Khamisu Ahmad Mailantarki, wanda ya nemi tikitin takarar gwaman Gombe, ya zargi Farfesa Isa Ali Pantami da rashin adalci a siyasar jihar. Mailantarki ya ce Pantami ya bar harkar malanta ya koma neman mabiya, inda ya yi ikirarin cewa yawancinsu ba ’yan Gombe ba ne. Dan siyasar ya ce Pantami ya fi shi a ilimin addini, amma a siyasa ya fi shi gogewa, saboda ya taba zama ɗan majalisa da minista
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Pantami, Gombe - Wanda ya nemi tikitin takarar gwamnan Gombe, Hon. Khamisu Ahmad Mailantarki ya yi magana kan siyasar jihar.
Mailantarki ya bayyana rashin jin dadi kan yadda Farfesa Isa Ali Pantami ya yi masu rashin adalci.

Source: Facebook
Dan siyasar ya bayyana haka ne a cikin wani bidiyo da shafin DCL Hausa ta wallafa a Facebook a yau Lahadi 13 ga watan Satumbar 2026.
'Mun yi mamakin halin Isa Pantami'
A cikin bidiyon, Mailantarki ya ce ba su yi tsammanin haka daga malami kamar Isa Ali Pantami ba saboda mutuncinsa da suke gani.
Ya ce Pantami ya bar layin malanta ya koma neman mabiya wadanda mafi yawansu ba ƴan Gombe ba ne domin haka ya kamata ya gyara siyasarsa.
Ya ce:
"Yanzu abin da malam ke yi, ya bar harkar malanta ya koma neman mabiya, in ba haka ba, a haka zaka ci zabe.
"Ai a Gombe ake zabe, magoya bayanka kaso 95 ba ƴan Gombe ba ne.
"A yau idan ya wallafa wani abu a Facebook ku duba ki gani, yawanci masu sharhi kaso 99 ba yan Gombe ba ne."
Mailantarki ya faɗi bangaren da ya fi Pantami
Mailantarki ya bayyana cewa Isa Ali Pantami ya fishi a fannin addini amma ko kadan ba zai kama hannunsa a bangaren siyasa ba saboda gudunmawar da ya bayar kuma ya ke ci gaba da bayarwa.
Ya ce ya yi dan majalisar wakilai kuma ya yi takarar gwamna har sau uku amma rana daya ya zo ya ce yafi kowa cancanta.
"A ilimin addini yana gaba na, amma a siyasa ina gabansa, na yi mamba a majalisar wakilai kuma minista yana kasa da dan majalisar wakilai.
"Na yi takarar gwamna ba sau daya ba, an yi zaɓe da har sau uku amma ka zo rana daya ka ce ka fi kowa cancanta sauran ba su cancanta ba.
"Wannan cin mutunci ne kuma ya yi mana kage kuma bai kyauta mana ba, kuma a matsayinsa na malami ba mu yi tsammanin haka daga gare shi ba."
- Khamisu Ahmad Mailantarki
Tsohon Kwamishina ya shiga layin Pantami
A baya, an ki cewa tsohon kwamishinan Gombe, Muhammad Ismail City ya fice daga APC tare da bayyana goyon bayansa ga Isa Ali Pantami a zaɓen gwamna na 2027.
Tsohon shugaban Ƙaramar Hukumar Akko ya ce Gombe na buƙatar shugaba mai mutunci da ƙwarewar zamani ta duniya.
Muhammad ya bayyana Pantami a matsayin jagora mai hangen nesa da ƙwarewar sauya tsarin mulki da ci gaban tattalin arziki.
Asali: Legit.ng

