Ana Shirin Zaben 2027, Gagarumar Matsala Ta Tunkaro Hukumar INEC
- SERAP ta bai wa INEC kwana bakwai ta yi bayani kan sama da Naira biliyan 126 da aka ce an karkatar, ɓata ko kuma ba a yi bayaninsu ba
- Ƙungiyar ta nemi INEC ta bayyana waɗanda suka karɓi kuɗin, kwangiloli da kuma shaidar isar da kayayyakin da aka saya
- SERAP ta kuma buƙaci a miƙa zarge-zargen almundahana ga EFCC da ICPC domin gudanar da bincike da dawo da kuɗaɗen
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ƙungiyar Socio-Economic Rights and Accountability Project (SERAP) ta bai wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) wa’adin kwana bakwai ta yi bayani kan sama da Naira biliyan 126.46.
SERAP ta ce kuɗaɗen an ware su ne domin gudanar da harkokin zaɓe, amma rahoton binciken kudi ya nuna ana zargin an karkatar da su, an yi asara, an yi amfani da su ba bisa ka’ida ba ko kuma ba a yi bayaninsu ba.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan Asabar, 12 ga Satumba 2026 kuma mataimakin daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, ya sanya wa hannu wadda aka sanya a shafin X.
Kuɗaɗen sun shafi sayen akwatunan zaɓe, na’urorin zaɓe da kayayyakin gudanar da zaɓe, takardun zaɓe da sakamako, motoci da na’urorin tantance masu kaɗa ƙuri’a.
Haka kuma, sun haɗa da kuɗaɗen ayyukan binciken kuɗi, shawarwari, adana bayanai ta hanyar zamani da sauran kayayyaki da ayyukan da ake buƙata wajen gudanar da zaɓe.
Rahoton mai binciken kudi ya gano matsaloli
A cewar SERAP, rahoton binciken kuɗaɗen gwamnati na 2023 da mai binciken kudi na Tarayya ya fitar kuma aka wallafa a ranar 7 ga Agusta 2026, ya ƙunshi wasu abubuwan da suka faru tsakanin Janairu da Disamba 2022.
Ƙungiyar ta ce wasu daga cikin abubuwan da aka gano sun kuma kai har zuwa 31 ga Disamba 2023.
SERAP ta nemi Farfesa Joash Amupitan da INEC su bayyana yadda aka kashe sama da Naira biliyan 126, ciki har da adadin kuɗin da aka biya da waɗanda suka karɓe su.
Ta kuma nemi a bayyana kwangilolin da aka bayar, yadda aka gudanar da tsarin sayen kayayyakin, kamfanoni da masu samar da kayayyakin da abin ya shafa.
Haka kuma, ta nemi a gabatar da shaidar cewa an samar da kayayyakin, yadda aka yi amfani da su da kuma inda suke a halin yanzu.
SERAP ta nemi EFCC da ICPC su binciki lamarin
SERAP ta kuma buƙaci Amupitan da INEC su miƙa zarge-zargen karkatar da kuɗaɗe, kashe kuɗi ba bisa doka ba, take dokokin sayayya da sauran laifukan kuɗi ga Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC da ICPC.
Ƙungiyar ta ce hakan zai ba hukumomin damar gudanar da bincike, gurfanar da waɗanda suka dace tare da dawo da duk wani kuɗi da aka samu an biya ba bisa ka’ida ba.
Ta kuma nemi a gano jami’an gwamnati, ’yan kwangila, kamfanoni, masu samar da kayayyaki da masu ba da shawara da ke da hannu, tare da ɗaukar matakan dawo da kuɗaɗen.

Source: Facebook
INEC ta fitar da jerin sunayen 'yan takara
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar zabe ta INEC ta fitar da jerin sunayen ƙarshe na ’yan takarar zaɓen shugaban ƙasa da na Majalisar Dokoki ta Ƙasa a zaben 2027.
Jerin ya ƙunshi jam’iyyun siyasa 18 da ’yan takarar shugaban ƙasa da mataimakansu a zaben wanda za a gudanar a watan Janairu.
Asali: Legit.ng


