Daukar Doka Hannu: Matasa Sun Kashe Tsoho Dan Shekara 80 Bisa Zargi Aikata Maita

Daukar Doka Hannu: Matasa Sun Kashe Tsoho Dan Shekara 80 Bisa Zargi Aikata Maita

  • Wasu matasa sun kashe wani tsoho dan shekara 80 Ordue Ikye a jihar Benue bisa zarginsa da maita
  • Kungiyar AfAW ta aika takardar kuka ga kwamishinan yan sanda don gudanar da bincike kan lamarin
  • Zargin ya samo asali ne bayan mutuwar wani matashi mai suna Aker Aleva mai shekaru 30 a kauyen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Benue - Fusatattun matasa sun yiwa wani tsoho dan shekara 80 dukan mutuwa mai suna Ordue Ikye a karamar hukumar Gwer East da ke jihar Benue bayan sun zarge shi da amfani da maita wajen kashe dangi.

Lamarin auku ne a garin Tse-Ikye da ke gundumar Gbemacha Council, Mbavior, Mbasar, biyo bayan mutuwar Aker Aleva, wani matashi mai kimanin shekaru 30 a duniya.

An kashe tsoho a Benue kan zargin maita
Yadda aka yiwa tsoho kisan gilla kan zargin maye ne
Source: Original

Yadda lamarin ya faru

Kungiyar kare hakkin wadanda ake zargi da maita ta AfAW ta mika takardar kuka ga Kwamishinan Yan Sandan jihar Benue domin a bincika ainihin abin da ya faru, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Ana cikin wahala a ƙasa, Atiku, Tinubu sun kwashi miliyoyin dala sun kashe a Amurka

A cewar takardar kukan wadda ma'aikacin kungiyar, Dr Leo Igwe ya sanya wa hannu, mamacin Aker Aleva ya fita kallon kallo ne kawai, amma a hanyarsa ta komawa gida sai ya fara korafin ciwon kai kafin daga bisani ya yanke jiki ya fadi.

An kai Aleva asibiti da ke Ikpayongo inda a can ne ya cewa dangi ga garinku nan, lamarin da ya kada zukatan jama'a.

Bayan mutuwarsa ne aka shiga zargin Ordue Ikye, wanda dangi ne ga mamacin, da cewa shi ne ya yi amfani da maita wajen kawo karshen rayuwar matashin.

Shaidan gani da ido

A cewar dan mamacin wanda ya kasance shaidan gani da ido, ya koma gida ne bayan ya ji hayaniya mai karfi, inda ya tarar da mutane sun taru suna yi wa mahaifinsa barazana da titsiye da tambayoyi.

Mutanen sun kunna wuta a gefe biyu na tsohon tare da matsa gana masa azaba kan ya amsa laifin kashe Aleva. Tsohon ya kaddamar da cewa bashi da masaniya a kan abin da ya samu matashin kuma bai san komai game da mutuwarsa ba.

Kara karanta wannan

Bayanai sun fito: An ji abubuwan da suka faru da Ɗan Shagamu kafin a kashe shi a Kano

Duk da cewa wasu daga cikin mutanen da ke wajen sun nemi a yi hakuri, wasu daga ciki sun dauki itatuwa suka ci gaba da dukansa har sai da ya numfasa na karshe.

Kiran daukar matakin doka

Kungiyar AfAW ta gano mutane biyar da ke tsakiyar wannan hari har da shugaban matasan al'ummar, bisa bayanan da shaidan gani da ido ya bayar.

Kungiyar ta bukaci rundunar yan sanda da ta gudanar da bincike mai zaman kansa tare da kare iyalai da shaidun lamarin daga barazana ko tsangwama.

AfAW ta nuna damuwa mai tsanani kan yadda rashin lafiya ko mutuwar ba-zata ke zamewa mutane hujjojin cin zarafi da kisan gillar tsofaffi a al'umma.

Ta nemi jami'an tsaro su dauki matakai na gaskiya don hana sake aukuwar irin wannan danyen aiki a gaba tare da tabbatar da cewa wadanda ke da hannu sun fuskanci hukuncin doka.

An kashe wani bisa zargin maita a Ebonyi

A wani labarin na daban, mun ruwaito muku yadda rundunar ‘yan sanda a jihar Ebonyi da ke Kudu maso Gabas ta kama mutane 17 da ake zargi da kona wani mutum bisa zargin maita.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An shiga cikin gida an kashe babban malamin Najeriya a ƙasar waje

Kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Lahadi, inda ya ce lamarin ya faru a ranar 3 ga Janairu, 2025.

Ana yawan samun ayyukan daukar doka a hannu a Najeriya, shin ko wannan na da nasaba da yadda hukumomin tsaron Najeriya ke gaza daukar mataki kan wasu lamurran?

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng