Bayan Hutawa a Landan, Tinubu Ya Shilla Kasar da Ya Fi Ziyarta Tun bayan Hawansa Mulki

Bayan Hutawa a Landan, Tinubu Ya Shilla Kasar da Ya Fi Ziyarta Tun bayan Hawansa Mulki

  • Shugaba Bola Tinubu ya isa Paris, Faransa, domin ci gaba da hutun shekara na makonni uku da ya fara a Turai
  • Mai girma Bola Tinubu ya bar Abuja ranar 30 ga Agusta 2026, inda ya fara hutunsa a London kafin ya wuce Paris
  • Tun bayan hawansa mulki, Tinubu ya ziyarci Faransa sau akalla 13, yayin da ya shafe sama da kwanaki 270 a ƙasashen waje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Paris, Faransa - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya isa Paris babban birnin Faransa, domin ci gaba da hutun shekara na makonni uku da yake yi a Turai.

Majiyoyi da ke kusa da shugaban sun tabbatar da cewa mai girma Tinubu ya isa birnin Paris ranar Lahadi, 13 ga watan Satumban 2026.

Tinubu ya tafi Faransa
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Jakadan Najeriya a Faransa, Ayodele Oke, ne ya tarbi shugaban bayan isarsa Paris, kamar yadda hotunan da aka fitar suka nuna, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Malam Murtala Bello ya faɗi shirinsu da aka kai wa Sheikh Lukuwa hari a Sokoto

Tinubu ya fara hutunsa a Landan

Shugaba Tinubu ya bar Abuja ranar Lahadi, 30 ga Agusta, 2026, domin fara hutun makonni uku a Turai.

London, babban birnin Birtaniya, ce zangonsa na farko, kafin daga bisani ya zarce zuwa Paris domin ci gaba da hutun.

A lokacin da aka sanar da tafiyar, mai ba shugaban shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya ce Tinubu zai dawo Abuja bayan kammala hutun.

Tinubu zai dawo domin yakin neman zaɓen 2027

Sanarwar ta bayyana cewa ana sa ran shugaban zai koma Abuja bayan hutun domin shiga harkokin yakin neman zaɓen babban zaɓen watan Janairun 2027.

Tafiyar Tinubu zuwa hutun ta zo ne mako guda bayan fitar da jerin sunayen kwamitin yakin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC.

A cikin jerin sunayen, an naɗa Tinubu a matsayin shugaban kwamitin, yayin da mataimakinsa, Kashim Shettima, aka naɗa mataimakin shugaban kwamitin.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: An samu bayanai kan makarantun firamare da sakandare da Tinubu ya halarta

Tinubu ya ziyarci Paris sau 13

Paris ta kasance ɗaya daga cikin biranen ƙasashen waje da Shugaba Tinubu ya fi yawan ziyarta tun bayan hawansa mulki.

Tun lokacin da ya zama shugaban Najeriya a watan Mayun 2023, Tinubu ya ziyarci Paris aƙalla sau 13, inda ya shafe sama da kwanaki 50 a lokuta daban-daban na ziyarar aiki, tarurruka da kuma wasu tafiye-tafiye na kashin kansa.

Wata ƙididdigar dukkan tafiye-tafiyen shugaban zuwa ƙasashen waje da The Punch ta gudanar ta nuna cewa Tinubu ya shafe sama da kwanaki 270 a wajen Najeriya.

Rahoton ya ce shugaban ya ziyarci aƙalla ƙasashe 30 cikin tafiye-tafiye 51 da suka haɗa da ziyarce-ziyarcen aiki da sauran tafiye-tafiye.

Haka kuma, Tinubu ya yi tafiyar kusan mil 260,000, yayin da lokacin da ya shafe a cikin jiragen sama ya haura sa'o'i 400.

Jirgin Tinubu ya sauka a Paris
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na Najeriya Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Tinubu ya samu goyon baya

A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar 'yan kabilar Igbo a jihohin Arewa 19 da Abuja ta amince da Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin wa’adin mulki na biyu a 2027.

Ƙungiyar ta kuma yi alkawarin tattara ƙuri’u miliyan biyu domin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng