Tashin Hankali: An Yaudari Makusancin Gwamna An Harbe Shi Har Lahira a Najeriya

Tashin Hankali: An Yaudari Makusancin Gwamna An Harbe Shi Har Lahira a Najeriya

  • An harbe Olalekan Ajagungbade, wanda ke cikin makusanta na siyasa ga Gwamna Ademola Adeleke, har lahira a jihar Osun
  • Rahotanni sun nuna cewa wasu mutane ne suka yaudari Ajagungbade zuwa tashar motoci a Ile-Ife, inda aka harbe shi a kai
  • Gwamna Ademola Adeleke ya umarci dakarun ‘yan sanda su kamo duk waɗanda ke da hannu a kisan domin su fuskanci shari'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Osun, Nigeria - Matashin dan siyasa, Olalekan Ajagungbade, wanda ya kasance makusancin Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya rsa rayuwarsa bayan an harbe shi.

Rahotanni sun ce Ajagungbade, wanda aka fi sani da "Sarki" a da’irar siyasa, an yaudare shi zuwa wata tashar motoci a Ile-Ife domin halartar wani taro, inda aka harbe shi a kai.

Adeleke.
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke a fadar gwamnatinsa da ke Osogbo Hoto: @AAdeleke01
Source: Facebook

Rikici kan tashoshin motoci a Osun

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An shiga cikin gida an kashe babban malamin Najeriya a ƙasar waje

Daily Trust ta ruwaito cewa marigayin na fafutukar karɓe iko da tashoshin motoci a jihar daga hannun shugaban ƙungiyar direbobin haya ta jihar Osun, Nurudeen Alowonle.

Bayan rasuwarsa, an samu tashin hankali a wasu sassan jihar ta Osun, amma tuni jami'an tsaro suka fara kokarin shawo kan lamarin.

A halin da ake ciki, Gwamna Adeleke ya umarci rundunar ‘yan sandan jihar Osun da ta gano tare da kama duk waɗanda ke da hannu a kisan.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mallam Olawale Rasheed, ya fitar, Adeleke ya umarci ƙungiyoyin da ke rikici da juna da su fice daga tashoshin motoci nan take.

Gwamnan ya kuma bayar da umarnin kafa tsarin kula da tashoshin motoci nan take domin dawo da doka da oda.

Yayin da ya yi kira ga jama’a da su kwantar da hankulansu, gwamnan ya umarci hukumomin tsaro da su dawo da zaman lafiya a dukkan tashoshin motoci tare da tabbatar da bin doka da oda a faɗin jihar.

Gwamnan ya ce zai bayar da umarnin zartarwa domin kafa tsarin kula da tashoshin motoci, wanda zai taimaka wajen dawo da da’a da tsari.

Kara karanta wannan

Kaico: An tsinci gawar budurwa a wani yanayi bayan ta yi faɗa da saurayinta a Kaduna

“Dole ne a tabbatar da doka da oda. Ba za mu kyautata wa kowa ba, domin za a gurfanar da duk waɗanda suka aikata laifin gaban shari’a. Muna kira ga jama’a da su kwantar da hankulansu.”

“Za mu tabbatar da dawo da zaman lafiya a dukkan tashoshin motoci da wuraren da abin ya shafa. Hukumomin tsaro sun samu umarnin tabbatar da dorewar zaman lafiya ko da me hakan zai ci,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa: “Muna sake dawo da Tsarin Kula da Tashoshin Motoci. Nan ba da jimawa ba zan bayar da umarnin zartarwa domin aiwatar da sabon tsarin kula da tashoshin motoci da garej-garej a faɗin jihar.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262