'Yan Kabilar Igbo Sun Yi Watsi da Obi, Sun Bayyana Dan Takararsu a Zaben 2027
- Ƙungiyar ’yan kabilar Igbo a jihohin Arewa 19 da Abuja ta bayyana dan takarar da take goyon baya a zaben shugaban kasa na 2027
- Ta ce tana da akalla masu zaɓe miliyan biyu a jihohin Arewa da Abuja, waɗanda za su tallafa wajen samun nasarar APC a zaɓen
- Kungiyar ta kuma bayyana goyon bayanta ga ’yan takarar APC na gwamna da majalisu a jihohin Arewa da Babban Birnin Tarayya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Ƙungiyar siyasa ta Igbo Political Movement ƙarƙashin Igbo Delegates Assembly a jihohin Arewa 19 da Babban Birnin Tarayya, ta amince da Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin wa’adin mulki na biyu a 2027.
Ƙungiyar ta kuma yi alkawarin tattara ƙuri’u miliyan biyu domin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.

Kara karanta wannan
Magana ta kare, INEC ta fitar da sunayen yan takarar shugaban ƙasa na ƙarshe kafin zaben 2027

Source: Facebook
Darakta-Janar na Igbo Political Movement ƙarƙashin Igbo Delegates Assembly, Cif John Amaechi Onwe, ne ya bayyana hakan a ranar Asabar yayin wani taron manema labarai a Kaduna, cewar rahoton jaridar The Punch.
Haka kuma, ta bayyana goyon bayanta ga ’yan takarar APC da za su fafata a zaɓen gwamna da na majalisu a jihohin Arewa da Abuja.
Ƙungiyar ta bayyana matsayinta kan Peter Obi
Wannan sanarwar ta zo ne duk da cewa tsohon Gwamnan Anambra kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na Nigeria Democratic Congress (NDC) a 2027, Peter Obi, ɗan asalin ƙabilar Igbo ne.
Da aka tambayi Onwe matsayar ƙungiyar kan Obi, ya ce sun riga sun yanke shawarar goyon bayan Tinubu, yana mai jaddada cewa ba su dogara da la’akari da ƙabila wajen yanke shawarar ba.
“Mu da ke Arewa muna tare da Tinubu, babu wani abu da ya wuce haka,” in ji shi.
Dalilin goyon bayan Tinubu
Onwe ya ce ƙungiyar ta cimma wannan matsaya ne bayan gudanar da shawarwari da ’yan kasuwa, masana’antu, matasa, mata da shugabannin al’umma a faɗin jihohin Arewa 19 da Abuja.
Ya ce ƙungiyar ta kuma duba irin ayyukan da gwamnatin Tinubu ta gudanar cikin shekaru uku da suka gabata kafin ta yanke shawarar goyon bayan sake zaɓensa.
Ya bayyana cewa ƙungiyar, wadda ta ce ta yi imani da haɗin kan Najeriya, kasuwanci da ci gaba, za ta yi cikakken bayani wajen tallafa wa Tinubu a 2027.
Onwe ya ce suna da akalla masu kaɗa ƙuri’a miliyan biyu a jihohin Arewa 19 da Abuja, kuma za su yi amfani da wannan ƙarfin wajen neman nasarar Tinubu.

Source: Twitter
Sun yabawa ayyukan more rayuwa
Ƙungiyar ta kuma yabawa gwamnatin Tinubu kan ayyukan raya ababen more rayuwa da take gudanarwa, ciki har da Babbar Hanyar Legas zuwa Calabar, Hanyar Enugu zuwa Fatakwal da hanyoyin shiga gadar Second Niger Bridge.
A cewar Onwe, waɗannan ayyukan na da matuƙar muhimmanci ga ’yan kasuwar Igbo saboda ingantattun hanyoyin sufuri za su sauƙaƙa jigilar kayayyaki.
Ya ƙara da cewa inganta hanyoyin sufuri zai taimaka wajen bunƙasa harkokin kasuwanci da ƙara zirga-zirgar kayayyaki tsakanin yankuna.
Ƙungiyar ta ce goyon bayan da ta bai wa Tinubu ya samo asali ne daga abin da ta bayyana a matsayin ci gaba da ayyukan gwamnatin tarayya, ba wai saboda ƙabila ko asalin ɗan takara ba.
INEC ta goyi bayan Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar INEC ta nemi Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da Atiku Abubakar ya shigar kan takardun shaidar karatun Shugaba Bola Tinubu.
Atiku wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, ya shigar da ƙarar yana zargin an gabatar da jabun takardu domin cancantar Tinubu ya tsaya takarar shugaban ƙasa.
Asali: Legit.ng

