Gwamna Ya Ware Malaman Musulunci Yana Biyansu duk Wata, Ya Fada Masu Irin Wa'azin da Za Su Yi

Gwamna Ya Ware Malaman Musulunci Yana Biyansu duk Wata, Ya Fada Masu Irin Wa'azin da Za Su Yi

  • Gwamnatin Katsina karkashin Gwamna Dikko Radda ta fara biyan malamai 7,525 alawus na wata-wata domin yada zaman lafiya
  • Haka zalika gwamnatin ta kuma ɗauki shugabannin unguwanni 6,662 domin ƙarfafa tsaro da tattara bayanan sirri
  • Gwamnati ta ce kusan kananan hukumomi 16 daga cikin 26 sun samu sauƙin matsalar ’yan bindiga a jihar Katsina

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina, Nigeria - Gwamnatin Jihar Katsina ta ɗauki malamai addini 7,525 tare da sanya su cikin tsarin karɓar alawus na wata-wata domin yaɗa saƙonnin zaman lafiya, kwanciyar hankali da zaman tare.

Gwamnatin karkashin Gwamna Dikko Radda ta yi haka ne a matsayin wani ɓangare na matakan da ba na yaƙi ba wajen magance matsalar ’yan bindiga da sauran ƙalubalen tsaro.

Gwamna Radda.
Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda yana jagorantar taron majalissr zartarwa Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda
Source: Facebook

Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Harkokin Gida na jihar, Dakta Nasiru Muazu Dan Musa, ne ya bayyana hakan a wata hira da jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

2027: ADC ta fito da bayani, an ji dalilin Atiku na ƙin sa hannu a yarjejeniyar zaman lafiya

Ya ce gwamnati ta fahimci muhimmiyar rawar da malaman addini ke takawa wajen yin tasiri ga al’umma da inganta zaman lafiya.

Wane aiki gwamnati ta ba malaman?

Muazu ya ce biyan alawus ɗin malaman na daga cikin wata babbar dabara da gwamnati ke amfani da ita domin haɗa ayyukan sojoji da sauran jami’an tsaro da matakan da suka shafi al’umma da tattalin arziƙi.

“Mun fahimci muhimmancin addini wajen magance ƙalubalen tsaro. A lokaci guda, mun ɗauki malamai aiki tare da sanya su cikin tsarin samun alawus na wata-wata.
"Akwai malamai 7,525 da ake biyansu domin su yaɗa zaman lafiya, kwanciyar hankali da zaman tare,” in ji Muazu.

Ya ce gwamnatin ta kuma ɗauki masu unguwanni 6,662, waɗanda ke karɓar alawus na wata-wata, domin ƙarfafa tattara bayanan sirri daga matakin al’umma da kuma shigar da jama’a cikin ayyukan tabbatar da zaman lafiya.

A cewarsa, gwamnati ta haɗa waɗannan matakai da ayyukan sojoji da ’yan sanda, na’urorin sa ido, tallafa wa hukumomin tsaro da sauran matakan da ake ɗauka domin dawo da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

DSS ta bankado shirin 'yan bindiga na kai hari manyan makarantu a Sokoto

Dikko Radda.
Mai girma gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Radda a fadar gwamnatinsa Hoto: Ibrahim Kaula Mohammed
Source: Facebook

An samu sauƙin matsalar ’yan bindiga

Kwamishinan ya ce matakan sun taimaka wajen rage matsalar ’yan bindiga, inda kusan ƙananan hukumomi 15 zuwa 16 daga cikin 26 da a baya suka fuskanci matsalar rashin tsaro yanzu suke samun kwanciyar hankali.

Ya ƙara da cewa an sake buɗe makarantu da kasuwanni a wasu al’ummomin da abin ya shafa, yayin da manoma ke ƙara komawa gonakinsu.

Gwamna Radda ya yi gargadi kan tsaro

A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina , Dikko Umaru Radda, ya bukaciNal’ummar jihar su guji siyasantar da kalubalen rashin tsaro.

Radda ya ce rashin tsaro kalubale ne da ya shafi kowa, wanda ke bukatar hadin kai, addu’a da hadin gwiwa, ba amfani da shi wajen neman wata riba ta siyasa ba.

Ya bayyana jihar Katsina a matsayin jihar da Allah ya albarkace ta da ’ya’ya maza da mata masu hazaka, wadanda suka bayar da gagarumar gudummawa ga Najeriya da sauran kasashen duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262