Ma'aikatan Najeriya Sun Jikawa Tinubu Aiki, Sun Rufe Dukkan Ma'aikatu
- Ma’aikatan gwamnati a matakin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi sun fara yajin aikin gargadi na kwana uku a faɗin Najeriya kan matsin tattalin arziki
- Ƙungiyar JNPSNC ta umarci ma’aikatan gwamnati su shiga yajin aikin daga tsakiyar daren Juma’a zuwa ranar Lahadi saboda gazawar gwamnati wajen amsa buƙatunsu
- Ƙungiyoyin sun buƙaci a rage farashin fetur zuwa N500 kan kowace lita, a amince da tallafin albashi ga ma’aikata tare da fara tattaunawar sabon mafi ƙarancin albashi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Ma’aikatan gwamnati a matakin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi sun fara yajin aikin gargadi na kwana uku a faɗin Najeriya kan abin da suka bayyana a matsayin tsananin wahalar tattalin arziki.
Ƙungiyar JNPSNC ta umarci dukkan ma’aikatan ma’aikatu, hukumomi da sassan gwamnati su bi umarnin yajin aikin.

Kara karanta wannan
Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar hutu saboda cikar Najeriya shekaru 66 da samun 'yanci

Source: Facebook
An fara yajin aiki a Najeriya
Vanguard ta wallafa cewa umarnin shiga yajin aikin na ƙunshe ne cikin wata takarda da Sakataren JNPSNC na ƙasa, Olowoyo Gbenga, ya aika wa shugabannin ƙungiyoyin da ke ƙarƙashin majalisar.
Takardar ta ce yajin aikin ya fara daga tsakiyar daren Juma’a, 2 ga Oktoba, kuma zai ci gaba har zuwa Lahadi, 4 ga Oktoba, 2026.
Ƙungiyar ta ce ya zama wajibi ma’aikatan tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi su shiga yajin aikin saboda wahalar tattalin arziki da ta shafi ma’aikata da sauran ’yan Najeriya.
Me ma'aikata ke nema?
JNPSNC ta buƙaci gwamnatin tarayya ta rage farashin fetur zuwa N500 kan kowace lita domin rage matsin da hauhawar farashin man fetur ke jefa ma’aikata da sauran jama’a ciki.
Ƙungiyar ta kuma buƙaci gwamnati ta amince da tallafin albashi ga ma’aikatan Najeriya domin rage tasirin tsadar rayuwa.
Haka kuma, ta nemi kafa wani kwamiti mai wakilai daga gwamnati da ma’aikata domin fara tattaunawar sabon mafi ƙarancin albashi da ake sa ran fara aiki daga 2027.
JNPSNC ta ce gwamnati ta gaza
Punch ta wallafa cewa buƙatun sun biyo bayan wasiƙar da shugabannin JNPSNC suka aika wa Shugaba Bola Tinubu a ranar 21 ga Satumba, 2026.
Ƙungiyar ta ce ta bai wa gwamnati wa’adin zuwa ranar 30 ga Satumba domin ta ɗauki mataki kan farashin fetur, tallafin albashi da sauran matakan rage wahalar tattalin arziki.

Source: Twitter
Sai dai JNPSNC ta bayyana rashin jin daɗi bayan da jawabin Tinubu na bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin Najeriya bai yi magana kan buƙatunta na rage farashin fetur zuwa N500 ba.
Gargadin da JNPSNC ta yi
A wani labarin, mun ruwaito cewa JNPSNC ta gargadi gwamnatin tarayya kan wa’adin ranar 30 ga Satumba domin ta rage farashin fetur zuwa N500 ko ta shiga yajin aiki.
A cikin gargadi da ta yi, kungiyar ta ce tana kan bakar ta a kan buƙatar gwamnati ta fara tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashi ko ta fuskanci fushinta.
A lokacin, sakataren JNPSNC, Olowoyo Gbenga, ya ce wa’adin ranar 30 ga Satumba ba zai sauya ba, yana mai cewa ba za a ci gaba da yin watsi da damuwar ma’aikatan Najeriya ba.
Asali: Legit.ng
