'Yan Sanda Sun Yi Magana kan Hana Hawa a Kano bayan Kalaman Bangaren Aminu Ado

'Yan Sanda Sun Yi Magana kan Hana Hawa a Kano bayan Kalaman Bangaren Aminu Ado

  • Rundunar ’yan sandan Kano ta sake jaddada dakatar da yin hawa da hawan dawaki a wuraren jama’a, tana gargadin masu shirya irin waɗannan abubuwa su bi umarnin gwamnati
  • Kwamishinan ’yan sanda Ibrahim Adamu Bakori ya ce matakin ya samo asali ne daga damuwar tsaro da nufin kare zaman lafiya da doka
  • Duk wanda ke son gudanar da hawa ko hawan dawaki a wurin jama’a dole ya gabatar da rubutacciyar takarda ga ’yan sanda aƙalla sa’o’i 72 kafin taron

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Rundunar ’yan sandan Kano ta sake jaddada dakatar da gudanar da yin hawa da hawan dawaki a wuraren jama’a.

Rundunar 'yan sandan ta jihar Kano ta kuma gargadi masu shirya irin waɗannan abubuwa su bi umarnin.

Kara karanta wannan

Siyasa ta ɗauki zafi, 'yan daba dauke da bindigu sun buɗe wa magoya bayan PDP wuta

Kwamishinan 'yan sandan Kano ya yi jawabi
Kwamishinan 'yan sandan Kano na jawabi ga manema labarai Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manema labarai jawabi a hedikwatar rundunar da ke Bompai, Kano.

Ibrahim Adamu Bakori ya ce gwamnatin jihar ce ta sanya dokar dakatar da ayyukan, bayan tuntubar hukumomin tsaro da abin ya shafa.

Kwamishinan 'yan sandan ya ce manufar matakin ita ce kare zaman lafiya da tabbatar da bin doka da oda a jihar.

Damuwar tsaro na nan daram

Kwamishinan ya bayyana damuwa kan rahotannin cewa ana samun wasu mutane da ke karya umarnin dakatarwar.

Ya ce matsalolin tsaro da suka sa aka dauki matakin dakatar da yin hawa da hawan dawaki a wuraren jama’a har yanzu suna nan.

Rundunar ta kuma bukaci mazauna jihar da sauran masu ruwa da tsaki su fahimci cewa matakin na da nasaba ne da ƙoƙarin kare lafiyar jama’a.

Kara karanta wannan

Malamar addini ta fito ta gayawa Tinubu gaskiya kan halin da ake ciki a Najeriya

Sai an sanar da ’yan sanda kafin taro

Bakori ya ce wani taron haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro ya cimma matsaya cewa duk wani mutum, hukuma ko ƙungiya da ke son shirya hawa ko hawan dawaki a wurin jama’a dole ya gabatar da rubutacciyar takarda ga rundunar ’yan sanda.

Ya ce dole ne a gabatar da irin wannan buƙata aƙalla sa’o’i 72 kafin ranar gudanar da taron.

A cewarsa, hakan zai ba ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro damar gudanar da tantancewar tsaro tare da ɗaukar matakan da suka dace domin kare mahalarta da sauran jama’a.

An buƙaci jama’a su ba jami’an tsaro haɗin kai

Kwamishinan ya yi kira ga mazauna Kano, hukumomin gargajiya da masu shirya bukukuwa da su bi umarnin gwamnati tare da ba jami’an tsaro cikakken haɗin kai.

Ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa rundunar ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro za su ci gaba da yin duk abin da ya dace wajen kare rayuka da dukiyoyi.

Kara karanta wannan

Masifa ta auka wa masu hakar ma'adanai a Bauchi, an rasa rayuka

Bakori ya kuma ce jami’an tsaro za su ci gaba da aiki domin tabbatar da zaman lafiya a faɗin jihar Kano.

Yan sanda sun yi magana kan hawa a Kano
Taswirar jihar Kano, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sarki Aminu Ado ya yi korafi kan Sanusi II

A wani labarin kuma, kun ji cewa bangaren Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya mayar da martani bayan Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya hau doki zuwa wani taro duk da dokar hana yin hakan.

Sarkin Dawaki Babba kuma babban mamba a majalisar Sarkin Bayero, Aminu Babba Dan’agundi, ya ce sansanin Bayero na jiran ganin yadda gwamnatin jihar za ta mayar da martani kan matakin Sanusi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng