DSS Ta Bankado Shirin Yan Bindiga na Kai Hari Manyan Makarantu a Sokoto

DSS Ta Bankado Shirin Yan Bindiga na Kai Hari Manyan Makarantu a Sokoto

  • Hukumar DSS ta gargadi gwamnatin Sokoto kan shirin ’yan ta’adda da ’yan bindiga na kai hari cibiyoyin ilimi na gaba da sakandare a jihar
  • Hukumar ta ce sabbin bayanan sirri sun nuna cewa masu laifin na sauya salon ayyukansu daga makarantun firamare da sakandare zuwa jami’o’i
  • DSS ta bukaci a gaggauta karfafa tsaro a cibiyoyin ilimi domin kare dalibai, malamai, ma’aikata da sauran muhimman ababen more rayuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Sokoto – Hukumar DSS ta ce tana da bayanan sirri da ke nuna cewa ’yan ta’adda da ’yan bindiga na shirin kai hare-hare kan jami’o’i da sauran cibiyoyin ilimi na gaba da sakandare a fadin Jihar Sokoto.

Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata wasika mai dauke da ranar 18 ga Yuli, 2026, wadda aka aika wa gwamnatin Jihar Sokoto, kuma B. Abdulaziz ya sanya wa hannu a madadin Daraktan Tsaron Jihar.

Kara karanta wannan

Yadda sojoji suka ceto bayin Allah a Kebbi da wasu jihohi 2 daga yan bindiga

DSS ta gargadi gwamnati kan hari a Sokoto
Wasu jami'an DSS a bakin aiki Hoto: DSS Unofficial
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta kawo labarin cewa a cikin sanarwar tsaron, DSS ta ce sabon salon barazanar na iya haifar da mummunan tasiri ga harkokin ilimi idan ba a dauki matakan kariya cikin gaggawa ba.

DSS ta gargadi gwamnatin Sokoto

A ruwayar Daily post, hukumar ta ce bayanan da ta samu sun nuna cewa kungiyoyin masu aikata laifuka na sauya inda suke mayar da hankali, bayan da a baya suka fi kai hari kan makarantun firamare da sakandare.

DSS ta ce jami’o’i da sauran manyan makarantu na iya zama sabbin wuraren da ake niyyar kai hari saboda yawan dalibai, malamai, ma’aikatan makaranta da ’yan uwansu da ke wuraren.

A cewar hukumar, shirin ba wai kawai yin garkuwa da mutane yake nufi ba, domin yana iya kasancewa wani bangare na kokarin dakile harkokin ilimi.

Haka kuma hare-haren za su iya haddasa fargaba a tsakanin jama’a tare da rage amincewar mutane kan karfin gwamnati na kare rayuka da cibiyoyin gwamnati.

Kara karanta wannan

Gwamnan Sokoto ya gaya wa mutane abin da za su yi a kawo karshen 'yan bindiga

Kiran DSS ga gwamna Ahmed Aliyu

Hukumar ta kuma yi gargadin cewa samun nasarar kai hari kan manyan cibiyoyin ilimi na iya bata martabar Najeriya a idon kasashen duniya, tare da kara tabarbarewar yanayin rashin tsaro da ya addabi harkokin ilimi a wasu sassan kasar.

DSS ta tura sako ga gwamnatin Sokoto
Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto tare da Ministan tsaro Christopher Musa Hoto: Ahmad Aliyu Sokoto
Source: Facebook

Saboda haka, DSS ta bukaci a gaggauta inganta tsarin tsaro a kewayen jami’o’i da sauran manyan makarantu a Jihar Sokoto, tana mai cewa ya kamata a dauki matakan kariya tun kafin masu aikata laifin su kai farmaki.

Hukumar ta ce ta riga ta sanar da hukumomin tsaro da na bayar da agajin gaggawa da abin da ta gano, tare da bukatarsu da su dauki matakan da suka dace domin dakile hare-haren da ake zargin ana shiryawa.

Ta kuma bukaci gwamnatin Jihar Sokoto ta dauki gargadin da muhimmancin da ya dace, tare da gaggauta daukar matakai na hadin gwiwa domin karfafa tsaro a jami’o’i da sauran manyan makarantu.

Kwale-kwale ya kife a jihar Sokoto

Kara karanta wannan

Sojoji sun ɗana tarko, an daƙile harin garkuwa da mutane a Zamfara

A baya, mun kawo labarin cewa ana tunanin akalla mutum 40 sun rasa rayukansu bayan kwale-kwalen da ke ɗauke da manoma ya kife a Gorau, jihar Sokoto da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Yawancin mutanen da ke cikin kwale-kwalen yara ne masu shekaru tsakanin 10 zuwa 15 da haihuwa a duniya, lamarin da ya kara jefa jama'a a cikin tashin hankali da fargabar halin da ake ciki.

Rahotanni sun bayyana cewa da farko an samu nasarar ceto mutum shida ciki har da dagacin ​ƙauyen, yayin da ake ci gaba da aikin neman waɗanda suka ɓace ko za a same su da rai ko gawarwakinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng