Sabon Minista Zai Sa Kafar Wando da Kamfanoni, da Alamun Kudin Lantarki Ya Canza

Sabon Minista Zai Sa Kafar Wando da Kamfanoni, da Alamun Kudin Lantarki Ya Canza

  • Ministan wuta ya dauki damarar yaki da kamfanonin samar wa da na raba lantarki a Najeriya
  • Joseph Olasunkanmi Tegbe ya bayyana haka a wani jawabi da ya yi ranar 19 ga Agusta 2026
  • A taron NESG da aka yi, ministan ya fito da dabarun da za a bi domin gyara wutar lantarki a kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Ma’aikatar lantarki ta ce za ta hukunta kamfanonin wuta na DisCos da na GenCos da aka samu ba su aiki yadda ya dace.

Bugu da kari, Ma’ikatar tarayyar ta bayyana cewa za a kawo sauyi a tsarin farashin kudin wuta saboda a iya farfado da masana’antu.

Joseph Olasunkanmi Tegbe
Shugaban kasa tare da Joseph Olasunkanmi Tegbe da Sola Enikanolaiye bayan ya nada su ministoci Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Ministan wuta ya fito da tsare-tsaren shi

Vanguard ta ce Ministan wutan ya yi wannan bayani da yake gabatar da kundin tsare-tsare wajen taron NESG a ranar Laraba da ta wuce.

Kara karanta wannan

Babban balilin da ya sa Amurka ba za ta cire Najeriya daga jerin kasashen CPC ba

Joseph Olasunkanmi Tegbe ya gabatar da takardun ta hannun hadiminsa, Martins Olajide kuma an ga akwai alamun a ga canjin farashi.

Mista Joseph Olasunkanmi Tegbe ya ce za su fito da tsarin da za a rika amfani da shi wajen auna kokarin da kamfanonin wutan ke yi.

Daga kokarin da kamfanonin na GenCos da DisCos suka yi, za a rika ba su kyauta, kuma a tanadi ukuba ga marasa tabuka abin kirki.

Makasudin yin hakan shi ne a ceci masu shan wutan lantarki yayin da ake so a tabbatar da cewa ana samun wuta a kowane bangare.

Manufofin wutan sabon ministan lantarki

Sabon ministan ya fito da manufofi takwas da za a bi domin inganta harkar wuta, ba ‘yan kasuwa kwarin guiwa tare da karfafa aiki.

A cewar Joseph Olasunkanmi Tegbe, Najeriya tana da karfin samun megawatt 13, 625, amma abin da ake raba wa megawatt 4, 8454 ne.

Kara karanta wannan

Tsohuwar matar yaron El Rufai ta yi magana watanni shekaru 3 mutuwar aurensu

Abin da hakan yake nufi shi ne babu abin da ake yi da 62% na wutan da ake samarwa domin kamfanonin DisCos ba su iya raba shi.

Daga rahoton The Cable, an fahimci Mai girma ministan da aka nada a shekarar nan ya nuna ba zai yarda abubuwa su tafi a haka ba.

Wutar lantarki
Sabon Ministan lantarki, Joseph Olasunkanmi Tegbe Hoto: JosephTegbe/Instagram
Source: Instagram

Lantarki: Mutane suna nema wa kansu mafita

Wannan matsala da ake samu ta sa mutane a gidaje da ‘yan kasuwa sun rabu da kamfanonin lantarki, suna sama wa kansu wuta.

A haka ne ya ce ‘yan Najeriya sun kashe N16.5tr a shekarar 2023 alhali abin da aka samu daga tushen lantarkin kasa bai wuce N1tr ba.

Gwamnati ta kuma shaida cewa za ta dage wajen inganta karfin wuta ta layin Lagos, Enugu-Port Harcourt da kuma na Abuja-Kaduna-Kano.

Jihohi sun samu karin kudin yin ayyuka

An samu rahoto cewa Gwamnatin tarayya ta raba wa jihohi N435bn domin ayyuka na musamman a 2026 da ake kuka da rashin tsaro.

Jihohi 29 a Najeriya sun karbi N435bn tsakanin Janairu da Yuni 2026 domin tsaro da ayyukan raya kasa daga asusun FAAC a watanni shida.

Ana sa ran kudin su yi amfani wajen gina abubuwan more rayuwa da kuma tsare al'umma daga 'yan ta'adda sa masu garkuwa da mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng