Taraba: Sanatan APC ka Iya Rasa Takararsa kan Zargin Mallakar Takardun Bogi

Taraba: Sanatan APC ka Iya Rasa Takararsa kan Zargin Mallakar Takardun Bogi

  • Sanata David Jimkuta na fuskantar ƙorafin APC da ke neman a hana shi takarar 2027 bisa zargin gabatar da takardar NECO ta bogi
  • Janar Adamu Ibrahim mai ritaya, wanda ya sha kaye a zaben fidda gwani na APC, shi ne ya rubuta ƙorafin kan Jimkuta
  • Tsofaffin abokan karatun Jimkuta sun musanta zargin, inda suka tabbatar ya kammala karatu a GSS Wukari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jalingo, Taraba - Sanata David Jimkuta mai wakiltar Taraba ta Kudu na fuskantar ƙorafi da ke neman a hana shi takarar sanata a zaɓen 2027.

Ana zargin David Jimkuta da gabatar da takardun shaidar NECO na bogi ga jam’iyyar APC da kuma Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC.

Ana zargin Sanata da mallakar takardun bogi
Sanata David Jimkuta daga jihar Taraba. Hoto: Senator David Jimkuta.
Source: Facebook

Adamu Ibrahim, wani Manjo Janar mai ritaya, wanda ya sha kaye a hannun Jimkuta a zaɓen fidda gwani na APC, shi ne ya rubuta ƙorafin, cewar Premium Times.

Kara karanta wannan

Magana ta ƙare, INEC ta ɗora sabon tambarin jam'iyyar su Kwankwaso a shafinta

Ana zargin sanata da mallakar takardun bogi

Ƙorafin da aka sanya wa ranar 21 ga Satumba, an aika wa shugaban APC na ƙasa, inda Ibrahim ya zargi Jimkuta da gabatar da takardun bogi.

Ya kuma zargi sanatan da yin bayanan ƙarya a cikin takardun neman takara da ya gabatar wa jam’iyyar APC da INEC domin zaɓen 2027.

Ibrahim ya ce an haɗa takardun da ake zargin na bogi ne da takardar bayyana sha’awar Jimkuta da kuma fom ɗin neman takara.

Jimkuta shi ne sanatan da ke wakiltar mazabar Taraba ta Kudu a Majalisar Dattawa, kuma yanzu yana shirin sake neman kujerar a 2027.

Ana neman a hana sanatan APC takara kan zargin mallakar takardun bogi
Taswirar jihar Taraba da ke Arewa maso Yammacin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Abin da abokan karstunsa ke cewa

Sai dai tsofaffin ɗaliban Government Secondary School, GSS, Wukari, da suka kammala karatu a shekarar 2000 sun musanta zargin da ya shafi takardun karatunsa.

Tsofaffin abokan karatun sun ce sun koma makarantar ne domin duba bayanan da ke akwai bayan sun samu labarin ƙorafin da aka shigar.

Kara karanta wannan

Dan takarar PDP, wasu 3000 sun yi watsi da jam'iyyunsu, sun koma APC

Haruna Magaji, ɗaya daga cikin ɗaliban shekarar 2000, ya ce sunan Jimkuta yana matsayi na 98 cikin jerin ɗaliban da suka kammala karatu.

Magaji ya ce sun sake ziyartar GSS Wukari domin tabbatar da zargin da Janar Ibrahim ya yi wa sanatan, cewar Punch.

Ya ce sun tattara bayanan makarantar tare da yin cikakken bincike, inda suka gano cewa sunan Sanata David Jimkuta yana matsayi na 98.

Ƙungiyar tsofaffin ɗaliban ta ce David Jimkuta ya kammala karatu tare da su a shekarar 2000, kuma su ne rukunin farko da suka rubuta jarrabawar NECO.

Daga cikin abokan karatun akwai Zakaria Luka, Emmanuel Audu, Manasseh Wunuji, Haruna Magaji da Habibu Isyaka, kamar yadda aka bayyana a Jalingo.

Sai dai tabbatar da cewa Jimkuta ya halarci GSS Wukari kuma ya kammala karatu a can ba ya tabbatar da ingancin takardar NECO da aka gabatar.

Takardun bogi: An ba da belin tsohon minista

Kun ji cewa Babbar Kotun Tarayya ta fara sauraron shari'ar tsohon Ministan Bola Tinubu kan zarge-zarge shida da suka shafi amfani da takardun karatu na bogi.

Kara karanta wannan

Zaɓen 2027 da magana: Goodluck Jonathan ya fara yi wa APC 'aiki'

Gwamnatin Najeriya na zarginsa Uche Nnaji da gabatar da takardun digiri da na NYSC na bogi da kuma karɓar albashi ta hanyar yaudara.

Ana tsaka da wannan dambar ne sai Uche Nnaji ya yi murabus daga kujerarsa ta ministan kirire-kirkire da fasaha gabanin a kai shi kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.