Da Gaske Akwai Hujjar Peter Obi Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa na 2023?

Da Gaske Akwai Hujjar Peter Obi Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa na 2023?

  • Peter Obi ya amince cewa ba shi da wata hujja da zai gabatar don tabbatar da ikirarinsa na cewa ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2023
  • Tsohon gwamnan Anambra ya ci gaba da cewa ya yi amanna shi ne ya lashe zaɓen, duk da cewa kotuna sun yi watsi da ƙalubalensa
  • Obi ya kuma ce matsayinsa kan tallafin man fetur bai sauya ba, yana mai cewa cin hanci da rashawa ne babbar matsalar tsarin tallafin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Labour Party, Peter Obi, ya ce babu wata hujja da zai gabatar da za ta tabbatar da ikirarinsa na cewa shi ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Sai dai tsohon gwamnan jihar Anambra ya ci gaba da cewa ya yi amanna cewa shi ne ya lashe zaɓen.

Kara karanta wannan

Umahi: Minista ya raba gardama, ya fadi abin da zai sa Tinubu ya zarce a 2027

Obi ya yi magana kan zaben 2023
Peter Obi na jawabi a wajen taro Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Facebook

Obi ya bayyana hakan ne a wata hira da tashar BBC, yayin da yake magana kan ikirarinsa cewa an tafka magudi a zaɓen shugaban ƙasar na 2023.

Obi ya ce babu hujjar da zai gabatar

Da aka tambaye shi ko yana da hujjar da za ta tabbatar da cewa ya lashe zaɓen, Obi ya fara da cewa ba shi da ita.

“Babu hujja. Ba komai ake dogara da hujja ba,” in ji shi.

Sai dai nan take ya sake jaddada matsayinsa, yana cewa: “Na lashe zaɓen, kuma inan kan baka na.”

Ya ci gaba da cewa an tafka magudi a zaɓen 2023

An kuma tambayi Obi kan yadda yake ci gaba da cewa an tafka magudi a zaɓen 2023, duk da cewa kotuna sun yi watsi da ƙalubalen da ya shigar kan sakamakon.

“Ba na son komawa baya. Ina nan kan abin da na faɗa,” in ji Obi.

Kara karanta wannan

Mailantarki: Abokin hamayyar Pantami ya zo da sabon batu kan zaben fitar da gwanin PDP

A sakamakon da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ayyana, Bola Tinubu na All Progressives Congress (APC) ne ya lashe zaɓen.

Atiku Abubakar na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya zo na biyu, yayin da Obi ya zo na uku.

Obi da Atiku sun ƙalubalanci sakamakon zaɓen a Kotun Ƙoli ta Ƙasa mai sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa, amma kotun ta yi watsi da ƙarararsu. Daga bisani, Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasarar Tinubu.

Obi ya yi magana kan tallafin man fetur

A yayin hirar, Obi ya kuma yi magana kan matsayinsa game da tallafin man fetur, yana cewa matsayarsa ba ta sauya ba duk da sukar da ake yi masa kan cewa kalamansa game da batun sun sauya.

“Ban sauya ba. Abin da ya sauya shi ne duk lokacin da nake magana kan yadda za a aiwatar da shi, sai mutane su ce, ‘oh, ya sauya,’” in ji shi.

Ya ce tun farko matsayinsa ya ƙunshi damuwa kan cin hanci da rashawa da ke tattare da tsarin tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya bayyana halin Tinubu da ba zai dauka ba idan ya zama shugaban kaaa

“Na yi magana kan cin hanci da rashawa. Cin hanci da rashawa shi ne matsalar tallafin,” in ji Obi.
Peter Obi ya ce bai da hujja kan zaben 2023
Peter Obi mai neman shugabancin Najeriya a 2027 Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Facebook

An bukaci ka da a zabi Peter Obi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Anambra ta buƙaci magoya bayan jam’iyyar APGA da su kare tushen siyasarsu tare da bijire wa NDC da Peter Obi gabanin babban zaɓen 2027.

Gwamnatin ta zargi Peter Obi da kokarin rusa jam'iyyar APGA wadda ya rike mukamin gwamnan Anambra a cikinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng