Kamfanonin lantarki sun bada megawatt 5, 377 a farkon watan Agusta

Kamfanonin lantarki sun bada megawatt 5, 377 a farkon watan Agusta

Kamfanin TCN mai kula da samar da wutar lantarki a Najeriya, ya ce an samu megawatts 5, 377 na karfin wuta a farkon watan Agustan nan mai-ci.

A wani jawabi da kamfanin TCN ya fitar, ya ce Najeriya ta yi nasarar samun wadannan dinbin megawatt ne a ranar Asabar, 1 ga watan Agusta, 2020.

Kamar yadda jawabin ya nuna, wannan ne karon farko a tarihi da karfin wutan da aka samar ya kai wannan adadi.

Mafi yawan abin da aka taba samu a kasar nan shi ne 5, 375MW a shekarar da ta wuce. TCN ta ce wannan karo an samu karin kusan megawatts uku.

“Kamfanin wutan Najeriya ya na sanar da cewa ya samar da karfin lantarkin da ba a taba gani a tarihi ba, na 5,377.8 MW a ranar 1 ga watan Agusta, 2020 da karfe 9:30 na dare.”

“Wannan munzali da aka kai ya zarce abin da aka taba samu a ranar 7 ga watan Fubrairun 2019 da 2.8MW.” inji kamfanin TCN.

KU KARANTA: Za a samu karin 20, 000mw cikin shekara 2 a Najeriya - TCN

Kamfanonin lantarki sun bada megawatt 5, 377 a farkon watan Agusta
Injiniya Saleh Mamman
Asali: Twitter

Jawabin na TCN ya ce an yi nasarar aika wannan wuta zuwa tashoshin da ke da alhakin raba lantarki a fadin Najeriya.

Abin da Najeriya za ta iya ajiyewa na wutan lantarki shi ne 12,954MW, amma abin da ake da shi a yanzu haka a kasa bai zarce 7, 600MW.

Kamfanonin lantarki za su iya aika har 8,100MW, amma saboda wasu matsaloli da ake fuskanta, a lokaci guda karfin wutan da ake aikawa ba ya zarce 6, 000MW.

Jaridar The Cable ta ce su ma kamfanonin da ke rabon wuta ba su iya daukar lantarkin da ya wuce 5, 000MW. Yin hakan zai iya sa na’urorin kamfanonin DisCos su tashi aiki.

Ministan wutan lantarkin Najeriya, Injiniya Saleh Mamman, ya tabbatar da wannan tarihi da aka kafa. Mamman ya fitar da jawabi a shafinsa na Twitter.

Mamman ya ce an yi dace wajen tura wannan wuta zuwa tashoshin kasar. Ministan ya yabawa ma’aikatan da su ka yi kokari wajen ganin an kafa wannan tarihi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel