Hukumar Kwastam Ta Kafa tarihin tatso N28.1bn a Rana 1 a Tashar Apapa
- Jami’an kwastam da ke sashen Apapa a jihar Legas sun tatso N28.1bn a rana guda, abin da ba a taba yi ba
- An samu wannan nasara ne makonni kalilan bayan umarnin ya tara kudaden shiga har N323bn a watan Yulin 2026
- Shugaban reshen, Emmanuel Oshoba, ya bayyana cewa kudin za su taimaka wajen gina ababen more rayuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Lagos - Hukumar kwastam ta reshen Apapa ta kafa sabon tarhin samu kudin shigan da ya kai N28.1bn a rana guda kurum.
Wannan makudan biliyoyi da aka samu ya zama tarihi, ya zarce wanda jami’an na kwastam suka kafa a atan Satumban 2025.

Source: Getty Images
Kwastam ta samu N28.1bn a tashar Apapa
Jaridar The Guardian ta rahoto cewa wannan sanarwa ta fito ne daga bakin Kakakin kwastam na reshen Apapa, Isah Sulaiman.
Isah Sulaiman shi ne Jami’in yada labarai na kwastam ya fitar da sanarwa yana cewa bayanin wannan nasara da aka samu.

Kara karanta wannan
Sojojin sama sun yi barin wuta kan yan ta'adda, miyagu da dama sun rasa rayukansu
CSC Isah Sulaiman yake cewa an kafa wannan tarihi ne makonni kadan bayan sun yi nasarar tattaro N323bn a watan Yulin 2026.
Jami'an kwastam a Apapa sun bar tarihi
Shugaban ‘yan kwastam na reshen, Emmanuel Oshoba ya ce wannan ne karon farko da aka taba samun N28.1bn a kwana guda.
Yake cewa nasarar ba ta kudin da aka samu ranar ba ce kawai, har da gudumuwar ma’aikatansa wajen inganta tattalin arzikin kasa.

Source: Getty Images
Daily Nigerian ta rahoto Oshoba yana bayanin yadda ake aiki da kudin da ake tatsowa wajen harkar ilmi, kiwon lafiya da sauran ayyuka.
Da wadannan kudi ne ake samar da abubuwan more rayuwan da jama’a ke samu a Najeriya.
An yabi aikin Bashir Adeniya a gidan kwastam
Ma’aikatan kwastam din na Apapa sun sadaukar da wannan nasara ga gwamnati da 'yan Najeriya tare da jinjina wa CG Bashir Adeniyi.
Ana ganin kokarin Shugaban kwastam na kasa, Bashir Adeniyi da ‘yan majalisarsa sun zamanantar da sha’anin tattaro kudin-shiga.
A shekarar 2023 ne Bola Tinubu ya amince da nadin Bashir Adewale Adeniyi zama shugaban kwastam bayan shekaru yana aiki.
Bashir Adeniyi ya canji Hameed Ali da ya rike kujerar nan a lokacin Muhammadu Buhari.
Oshoba ya ce dabarun da Adeniyi ya kawo a ofis sun yi rawar gani wajen saukaka ayyukan kwastam da saukaka aiki a kan iyakokin kasa.
Shugaban kwastam din ya yi kira ga jami’ansa da cewa kada su yi sanya, wannan tarihi da aka kafa ya zama hanyar zaburar da su.
Gwamnatin tarayya za ta yi ayyukan tituna
Karamin ministan ayyuka ya ce Gwamnatin tarayya ta yarda a batar da ₦430bn a ginin tituna da tasha kamar yadda aka ji labari jiya.
Majalisar ministoci ta yarda a kashe kudin wajen yin tituna a Ekiti, Ogun da Rivers da kuma gina wuraren ajiye motocin kaya a jihar Abia.
Bello Goronyo ya sanar da hakan ne a karshen zaman da majalisar ministoci ta yi bayan tsawon lokaci ba a yi zaman na FEC ba.
Asali: Legit.ng
