'Ku yi watsi da ɗan siyasar da bai ɗaga wayarku': Sarki ya ba mutane shawara

'Ku yi watsi da ɗan siyasar da bai ɗaga wayarku': Sarki ya ba mutane shawara

  • Sarkin Iselu, Oba Akintunde Akinyemi, ya bukaci al’ummar Ogun su ki zaben ’yan siyasar da ba sa amsa kiransu ko sakonninsu
  • Sarkin ya ce rashin sadarwa tsakanin shugabanni da jama’a na iya haifar da rashin amincewa da jita-jita
  • Oba Akinyemi ya bukaci sarakuna, ’yan siyasa da masu kada kuri’a su dauki amsa kira da sakonni a matsayin muhimmin tsarin shugabanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Iselu, Ogun - Sarkin Iselu na masarautar Iselu da ke karamar hukumar Yewa ta Arewa a jihar Ogun, Oba Akintunde Akinyemi, ya bukaci mazauna jihar su ki zaben ’yan siyasar da ba sa amsa kiransu da sakonninsu.

Oba Akinyemi ya kuma shawarci sarakunan gargajiya, hakimai, ’yan siyasa, kungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki su dauki sadarwa tsakanin masu rike da mukaman gwamnati da jama’a da muhimmanci.

Kara karanta wannan

Doguwa ya fito da abubuwa 2 da za su ceci APC daga shan kaye a jihar Kano a zaben 2027

Sarki ya shawarci mutanensa kan zaben 2027
Sarkin Iselu a jihar Ogun, Oba Akintunde Akinyemi. Hoto: GlobalScope.
Source: Facebook

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, Oba Akinyemi ya ce rashin ingantacciyar sadarwa daga masu rike da mukaman gwamnati na iya haifar da wani “gibin bayanai” da zai iya lalata amincewar jama’a da halaccin siyasa, cewar The Nation.

Matsalar da ke faruwa tsakanin shugabanni, mabiya

Sarkin ya ce gibin sadarwa tsakanin shugabanni da jama’a na iya rage amincewar jama’a da gwamnati, tare da haddasa yada bayanan karya da kuma raunana tsarin mulki.

Ya ce mutanen da ba sa iya tuntubar shugabanninsu na iya fara zargin manufar shugabannin, tare da daukar shirunsu a matsayin kokarin boye wasu abubuwan da ba su dace ba.

Oba Akinyemi ya ce idan jami’in gwamnati ya kasa sadarwa da mutanensa, hakan na iya haifar da gibi mai hatsari da zai lalata amincewar jama’a, ya yada labaran karya tare da kawo cikas ga shugabanci.

Sarkin ya kara da cewa rashin sadarwa na iya haifar da rugujewar amincewa da rasa kwarin gwiwar jama’a, lamarin da zai sa su ji shugabanninsu sun yi watsi da su.

Kara karanta wannan

Tinubu ko Atiku: An yi hasashen wanda zai lashe zaben 2027 daga Turai

Ya kuma ce zargin cin hanci da rashawa na iya karuwa sakamakon rashin sadarwa, saboda shirun jami’in gwamnati na iya fassaruwa a matsayin alamar laifi, boye-boye ko kokarin boye ba daidai ba.

Sarki ya shawarci yan siyasa a Ogun
Taswirar jihar Ogun da ke Kudancin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Gargadin da Sarkin ya yi ga al'umma

Sarkin ya yi gargadin cewa matsalar za ta iya kara tsanani yayin lokutan gaggawa, inda rashin sadarwa zai iya ta’azzara rikice-rikice, haddasa fargaba da kuma rage bin umarnin gwamnati.

Ya ce amsa kira da sakonnin jama’a ya kamata a dauke shi a matsayin muhimmin nauyin duk wanda ke rike da mukamin gwamnati ko kuma ke neman takarar zabe, cewar rahoton Punch.

Akinyemi ya ce duk wani jami’in gwamnati ko dan takarar jam’iyyar siyasa da ya mayar da kansa ba ya samuwa ga jama’a bai cancanci kuri’ar sarakunan gargajiyar Ogun ko ta al’ummar jihar ba.

Yan adawa sun koma APC a Ogun

A wani labarin, an ji cewa wasu tsofaffin magoya bayan PDP da ADC a Ogun sun fara gangamin neman goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu da Sanata Solomon Olamilekan Adeola.

Kungiyar Yayi Ni Wura Alliance Movement ta ce tana shirin tattara kuri'u 100,000 ga jam'iyyar APC a zaben 2027 a jihar Ogun.

Kungiyar ta ce mambobinta sun fito daga bangarorin siyasa daban-daban, kuma za su gudanar da gangamin ne ta hanyar tuntubar jama'a da ayyukan al'umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.