An Yi wa Tsohuwar Shugabar Matan APC Kisan Gilla a Gidanta da ke Bauchi
- An kashe tsohuwar shugabar mata ta APC a Bauchi, Jamima J. Dutse, bayan wasu da ba a san ko su waye ba sun kai mata hari gidanta
- Kungiyar Take-It-Back Movement ta yi Allah-wadai da kisan, tare da neman ’yan sanda, DSS da sauran hukumomin tsaro su gaggauta gudanar da bincike
- Kungiyar ta bukaci a kafa kwamitin bincike na musamman, tare da cafke wadanda suka aikata kisan domin su fuskanci hukunci da kuma tabbatar da adalci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Bauchi - Ana zargin wasu yan daba sun yi wata matar kisan gilla a gidanta da ke Bauchi wanda ake alaƙantawa da siyasa.
An kashe tsohuwar shugabar mata ta jam’iyyar APC a Bauchi ta Kudu, Jamima J. Dutse, bayan wasu da ba a san ko su waye ba sun kai mata hari a gidanta da ke Bauchi.

Kara karanta wannan
Ba ɓoye ɓoye, Gwamna Sule ya faɗi jihohi 3 da APC ke fuskantar babban ƙalubale gabanin 2027

Source: Original
Hakan na cikin wata sanarwa da kungiyar Take-It-Back Movement reshen jihad Bauchi wanda shugabanta, Nazif Bashi ya wallafa a shafin Facebook.
Kungiyar ta yi Allah-wadai da kisan, tare da neman hukumomin tsaro su gaggauta bincike domin gano wadanda suka aikata kisan.
Ta jajanta wa iyalan Dutse, abokanta da sauran makusantanta, tana mai bayyana kisan a matsayin mummunan aikin ta’addanci da ke barazana ga tsaron al’ummar jihar.
Kungiyar ta ce rashin samun damar da ‘yan kasa ke yi na jin tsaro a gidajensu, ba tare da la’akari da siyasa ko jinsi ba, na da matukar damuwa.
Ta ce harin ba wai kawai an kai shi kan Dutse da iyalanta ba ne, har ila yau ya shafi zaman lafiya, tsaro da tsarin dimokuradiyya na jihar Bauchi.
Take-It-Back Movement ta bukaci rundunar ’yan sandan jihar Bauchi, DSS da sauran hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen gano tare da cafke wadanda ke da hannu.

Kara karanta wannan
Babbar magana: An yi yunkurin kashe ɗan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a Najeriya
Kungiyar ta kuma bukaci a gaggauta kafa wani kwamitin bincike na musamman mai karfin iko domin gudanar da cikakken bincike kan kisan tsohuwar shugabar matan.
Haka kuma, ta bukaci hukumomin tsaro su rika sanar da iyalan marigayiyar da jama’a halin da ake ciki, tare da bayyana matakan da ake dauka da kuma ci gaban binciken.
Kungiyar ta jaddada cewa dole ne a tabbatar da adalci, tare da gurfanar da wadanda suka aikata kisan a gaban kotu domin su fuskanci hukuncin da ya dace.
Ta kuma yi kira ga gwamnatin jihar Bauchi da hukumomin tsaro da su karfafa matakan tsaro, sa ido da tattara bayanan sirri a cikin birnin Bauchi da kananan hukumomin da ke makwabtaka.
Kungiyar ta ce daukar irin wadannan matakai ya zama wajibi saboda abin da ta bayyana a matsayin karuwar hare-haren tashin hankali a jihar.
Haka kuma, ta yi kira ga kungiyoyin fararen hula, kungiyoyin kwadago, masu kare hakkin dan Adam da al’ummar Bauchi da su ci gaba da neman a yi wa lamarin adalci.
Take-It-Back Movement ta ce za ta ci gaba da kare hakkokin ’yan kasa, tsaronsu da neman adalci, tana mai cewa yin shiru yayin rashin tsaro na taimakawa wajen ci gaba da zalunci.

Kara karanta wannan
Siyasa ta ɗauki zafi, 'yan daba dauke da bindigu sun buɗe wa magoya bayan PDP wuta
Karin bayani na tafe....
Asali: Legit.ng