An Fara Murna da Gwamnatin Tinubu Ta Cika Alkawarin da Ta Daukarwa Sojojin Najeriya
- Dada Olusegun ya ce jami’an sojojin Najeriya sun fara karɓar sabon albashin da Shugaba Bola Tinubu ya amince da shi a watan Agusta.
- Ƙarin albashin ya kasance tsakanin kashi 30 zuwa 80, gwargwadon matsayi, kuma ya shafi kusan jami’an tsaro 250,000
- Sabon tsarin albashin ya fara aiki daga 1 ga Satumba, inda jimillar kuɗin albashin sojoji a shekara zai tashi zuwa N924bn
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Dada Olusegun, mai taimaka wa Shugaba Bola Tinubu na musamman kan kafafen sada zumunta, ya ce jami’an sojin Najeriya sun fara karɓar sabon albashin da aka ƙara musu.
Onyechi Anele, kakakin rundunar sojojin ƙasa, da wani jami’i a hedikwatar tsaro ta ƙasa, DHQ, sun tabbatar da hakan.

Source: Twitter
Jaridar TheCable ta kawo rahoton cewa, Onyechi Anele ta tabbatar mata da fara karbar sabon karin albashin ne a ranar Alhamis, 1 ga watan Oktoban 2026.

Kara karanta wannan
Amaechi ya hango barazanar da ke fuskantar 'yan adawa idan Tinubu ya zarce a 2027
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Olusegun ya ce ƙarin albashin zai taimaka wajen ƙara wa jami’an soji ƙwarin gwiwa wajen gudanar da ayyukansu.
"Zan iya tabbatar da cewa jami’an sojojin Najeriya sun fara karɓar sabon albashin da Shugaba Bola Tinubu ya amince da shi a watan Agusta.” In ji shi.
Ya ƙara da cewa sabon tsarin albashin na daga cikin muhimman matakan da ake sa ran za su ƙara wa sojojin da ke bakin daga ƙwarin gwiwa yayin da suke ci gaba da yaƙi da matsalar rashin tsaro.
Tinubu ya amince da ƙarin albashin sojoji
A watan Agusta, Shugaba Bola Tinubu ya amince da sabon tsarin albashi ga jami’an rundunonin sojojin Najeriya.
Bayo Onanuga, mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, ya bayyana cewa ƙarin albashin ya kasance tsakanin kashi 30 zuwa 80 bisa matsayi.

Kara karanta wannan
An sanya sabon lokacin yanke hukunci a shari'ar sojojin da suka yi yunkurin kifar sa Tinubu
Onanuga ya ce kusan jami’an tsaro 250,000 ne za su amfana da sabon tsarin, wanda ya fara aiki daga ranar 1 ga Satumba.
Yadda aka tsara ƙarin albashin
A cewar Onanuga, jami’an da suke sama da matsayin Kanal, ciki har da Birgediya-Janar, Manjo-Janar, Laftanar-Janar da Janar, za su samu ƙarin albashi na kashi 30.
Ya ce jami’an da suke daga matsayin Kanal zuwa ƙasa har zuwa warrant officer za su samu ƙarin kashi 50 cikin 100.
Haka kuma, sojojin da suke daga matsayin Private zuwa Staff Sergeant za su samu ƙarin albashi mafi girma, wanda ya kai kashi 80.
Kuɗin albashin sojoji zai kai N924bn
Mai taimaka wa shugaban ƙasa ya bayyana cewa sabon tsarin albashin zai ƙara jimillar kuɗin da gwamnati ke kashewa wajen biyan albashin jami’an rundunonin soji a shekara.
A cewarsa, kuɗin albashin da a baya yake N660bn a shekara zai tashi zuwa N924bn bayan fara aiwatar da sabon tsarin.

Source: Twitter
Sojoji sun samu nasara kan 'yan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa hedikwatar tsaron Najeriya ta ce an samu hare-hare 367 a wurare daban-daban da rundunar soji ke gudanar da ayyuka a fadin ƙasar cikin watan Satumba 2026.
Sojoji sun ce sun kama ’yan ta’adda da masu aikata laifuffuka 350, sun ceto fararen hula 655 da aka yi garkuwa da su, sannan ’yan tawaye 75 sun mika wuya.
Asali: Legit.ng