Rundunar Sojoji Ta Nada Sabon Kwamandan da Zai Jagoranci Yaki da Boko Haram
- Rundunar sojojin Najeriya ta naɗa sabon kwamandan Operation Hadin Kai, inda ya maye gurbin Manjo Janar Abdulsalam Abubakar
- Sauyin kwamandan ya zo ne gabanin zaɓen shugaban ƙasa na watan Janairu, yayin da rashin tsaro ke ci gaba da zama babban ƙalubale
- Rundunar sojojin ta ce sauyin wani ɓangare ne na garambawul da ya shafi janar-janar 15 domin inganta ayyukan sojoji da tsarin jagoranci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Rundunar sojojin Najeriya ta naɗa sabon kwamandan da zai jagoranci ayyukan sojoji kan Boko Haram da ISWAP a Arewa maso Gabas.
Sabon kwamandan, Manjo Janar Ibikunle Ademola Ajose, ya maye gurbin Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, wanda shi ne kwamanda na 15 na Operation Hadin Kai.

Source: Facebook
Ajose ya maye gurbin Abdulsalam Abubakar
Mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya, Kanal Appolonia Anele ta bayyana sauyin ne cikin wata sanarwa ranar Laraba, 9 ga watan Satumban 2026 a shafin Facebook.

Kara karanta wannan
Janar Christopher Musa ya kira ruwa, lauyoyin El Rufai sun nemi N10bn da wasu bukatu
Ajose, wanda a baya ya yi aiki a hedikwatar rundunar sojoji da ke Abuja, ya karɓi ragamar Operation Hadin Kai daga Abdulsalam Abubakar, wanda ya fara jagorantar aikin a watan Afrilun 2025.
Sauyin kwamandan ya zo ne ƙasa da shekaru biyu bayan naɗin Abdulsalam Abubakar, yayin da ƙasar ke shirin tunkarar zaɓen shugaban ƙasa da ake sa ran gudanarwa a watan Janairu.
Rashin tsaro na ci gaba da zama ƙalubale
Naɗin sabon kwamandan ya zo ne a lokacin da matsalar tsaro ke ci gaba da zama babban abin damuwa gabanin zaɓen.
Shekaru da dama na hare-haren ’yan tada ƙayar baya, ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane sun shafi sassa daban-daban na Najeriya.
A cewar bayanan Armed Conflict Location & Event Data Project (ACLED), hare-haren Boko Haram da ɓangaren da ya balle daga cikinta, wato Islamic State West Africa Province (ISWAP), sun kashe sama da mutane 40,000 tare da raba miliyoyin mutane da muhallansu tun daga shekarar 2009.
Hare-haren Boko Haram sun shafi zaɓe
Matsalar tsaro ta kawo cikas ga gudanar da zaɓe a wasu sassan Arewa maso Gabashin Najeriya yayin zaɓen shugaban ƙasa na baya, cewar rahoton Reuters.
Rahoton ya ce har yanzu rashin tsaro na zama wani babban ƙalubale yayin da ake shirin gudanar da zaɓen shekara mai zuwa.
Sai dai rundunar sojin ba ta danganta sauyin kwamandan da wani hari na baya-bayan nan da aka kai a Arewa maso Gabas ba.
Sauyin ya shafi janar-janar 15
A cewar sanarwar mai magana da yawun rundunar soji, Appolonia Anele, sauyin wani ɓangare ne na babban garambawul da ya shafi wasu janar-janar 14 ban da sabon kwamandan.
Ta ce an gudanar da garambawul ɗin ne domin inganta tasirin ayyukan soji, ƙarfafa jagoranci da kuma daidaita tsarin kwamandoji da sauye-sauyen ƙalubalen tsaron Najeriya.
Rundunar ta ce sabon tsarin jagorancin na da nufin tabbatar da cewa sojojin sun kasance cikin shiri yadda ya kamata domin tinkarar matsalolin tsaro da ke fuskantar ƙasar.

Source: Twitter
Sojoji sun kai hari Zamfara
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun runduna Operation Fansan Yamma sun kai farmakin sama kan wasu da ake zargi ‘yan ta’adda ne a yankin Yankuzo, Ƙaramar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara.
Majiyoyin yankin sun ce lamarin ya faru ne lokacin da jiragen yaƙin soji guda biyar suka gudanar da wani farmaki na haɗin gwiwa a yankin.
Asali: Legit.ng

