Bata Sunan OPay: Bashir Ahmad Ya Roki Alfarma kan Cafke Hafsat

Bata Sunan OPay: Bashir Ahmad Ya Roki Alfarma kan Cafke Hafsat

  • Tsohon hadimin shugaban ƙasa, Bashir Ahmad, ya tura alfarma ga kamfanin OPay bayan cafke wata yarinya kan yada karya
  • Bashir ya ce Hafsa ta amince da kuskurenta, ta goge sakon da ta wallafa kuma ta nemi afuwa kamar yadda OPay ya buƙata
  • Ya roƙi OPay ya saki Hafsat, yana mai cewa za a iya hukunta kuskurenta tare da nuna tausayi domin ka da abin ya lalata makomarta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Tsohon hadimin shugaban ƙasa, Bashir Ahmad, ya roƙi kamfanin OPay bayan cafke wata budurwa.

Bashir Ahmad ya roki Opay da ya sake duba batun kama Hafsat Abubakar, wacce aka tsare saboda yaɗa wani sakon ƙarya.

Bashir Ahmad ya magantu kan cafke Hafsat Abubakar
Matashiya Hafsat Abubakar da Bashir Ahmad. Hoto: Bashir Ahmad.
Source: Facebook

Dan siyasar ya yi wannan roƙon ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Alhamis 10 ga watan Satumbar shekarar 2026.

Kara karanta wannan

"A wasu lokutan," Ana zargin ba Shugaba Tinubu ke tafiyar da mulkin Najeriya ba

Bashir ya roki Opay kan cafke Hafsat

Bashir ya ce Hafsat ta amince da kuskurenta, kuma bisa fahimtarsa, ta bi umarnin OPay na goge sakon tare da neman afuwa.

Ya ce:

“Dukkanmu mun san abin da Hafsa ta aikata ba daidai ba ne, kuma kusan babu wanda ya goyi bayan abin da ta yi. Sai dai ina da tambayoyi kan abin da ya faru daga baya.
“Daga abin da na fahimta, bayan sakonta ya yaɗu sosai, OPay ya nemi kawai ta goge sakon tare da neman afuwa cikin wa’adin da aka ba ta. Fahimtata ita ce ta yi daidai abin da aka umarce ta; ta cire sakon kuma ta nemi afuwa.
“To, me ya sa OPay har yanzu zai ci gaba da neman a kama ta, musamman idan ta bi duk buƙatun kamfanin?”

Bashir ya ce da ya ɗauki lamarin da wani salo idan Hafsat ta ƙi goge sakon ko neman afuwa bayan an buƙaci ta yi hakan.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya kinkimo maganar kisan Sardauna, ya bayar da shawara

An kama wacce ta yada karya kan Opay
Hafsat Abubakar da sufeta-janar na yan sandan Najeriya. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Facebook

Rokon da Bashir Ahmad ya yi ga Opay

Tsohon hadimin shugaban ƙasar ya roƙi kamfanin OPay ya sake duba lamarin, yana mai bayyana Hafsat a matsayin matashiya kuma ɗaliba da ta yi kuskure, sannan ta bi matakan gyara da kamfanin ya buƙace ta.

Ya yi Allah wadai da abin da ta aikata yana mai cewa za a iya ɗaukar matakin ladabtarwa tare da nuna tausayi idan mutum ya amince da kuskurensa.

Ya ce:

“Za mu iya yin Allah wadai da abin da Hafsa ta aikata ba tare da yin Allah wadai da ita a matsayin mutum ba. Za mu iya riƙe mutane da alhakin kurakurensu tare da nuna musu tausayi, musamman idan sun amince da kuskurensu kuma suka bi matakin gyaran da aka buƙace su.”

Ya roƙi OPay ya saki Hafsat tare da barin lamarin ya zama darasi, maimakon ya haifar da illa ga makomar ɗalibar.

Opay ya musanta jita-jita da ae yadawa

Kara karanta wannan

An cafke Hafsat kan zargin yaɗa rahoton cewa Opay za su bar Najeriya

An ji cewa kamfanin hada-hadar kudi na OPay ya karyata rahotannin da ke cewa zai dakatar da ayyukansa daga ranar Talata, 1 ga Satumba, 2026.

Kamfanin ya ce babu wani shiri na dakatar da ayyukansa, yana mai tabbatar wa kwastomomi cewa za su ci gaba da amfani da ayyukansa.

OPay ya bukaci jama’a su rika tantance sahihancin bayanai kafin su yada su, musamman idan sun shafi kudade ko asusun banki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.