Karshen Alewa: Kotu Ta Kama Mutum 4 da Laifin Garkuwa da Mutane, Ta Yanke Masu Hukunci
- Babbar kotuna jihar Edo da ke Kudancin Najeriya ta yanke wa mutane huɗu hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan kama su da laifi
- Bayanai sun nuna cewa kotun ta same su da laifin garkuwa da mutane da kasancewa cikin ƙungiyoyin asiri a jihar Edo
- Fun farko an kama su kan satar wata mata a kasuwar Vegetable Market da ke Benin, kafin daga bisani a gurfanar d su a gaban kotu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Edo, Nigeria - Wata Babbar Kotu ta Musamman ta Jihar Edo da ke zama a Benin City, ta gamsu da hujjojin da aka gabatar mata, ga kama wasu mutum hudu da hannu a garkuwa da mutane
Sakamakom haka, babbar kotun ta yanke wa mutanen huɗu da aka samu da laifi hukuncin kisa ta hanyar rataya ranar Talata, 29 ga watan Satumba, 2026.

Source: Getty Images
Jaridar Tribune Nigeria ta ruwaito vewa mutanen huɗun, maza uku da mace ɗaya, an gurfanar da su a gaban kotun ne bisa zargin garkuwa da mutane da kasancewa mambobin ƙungiyoyin asiri.
Gwamnatin Edo ta kafa kotu ta musamman
Gwamnatin Jihar Edo ce ta kafa kotun musamman bayan yawaitar satar mutane, ayyukan ƙungiyoyin asiri da sauran laifuffukan tashin hankali a jihar watanni kaɗan da suka gabata.
Gwamna Monday Okoebholo ya ce matakin zai taimaka wajen dakile matsalar tare da aika saƙo mai zafi ga masu aikata laifuffuka cewa jihar Edo ba za ta zama mafaka gare su ba.
Mai girma gwamanan ya kuma sha alwashin cewa duk wanda aka kama da laifi, zai fuskanci hukunci daidai da abin da ya aikata bisa tanadin doka.
Kotu ta kama masu garkuwa da laifi
Rahotanni daga kotu ta musamman sun nuna cewa an kama waɗanda ake tuhumar ne dangane da satar wata mata da aka yi ranar 14 ga Yuni, 2026, a kasuwar kayan marmari da ke GRA na birnin Benin.

Kara karanta wannan
A ƙoƙarin sace shugaban ƙaramar hukuma, mutane fiye da 70 sun faɗa tarkon yan bindiga
Hukuncin, wanda ya ɗauki sama da sa’o’i uku, Mai Shari’a T. A. Momodu ya yanke shi kan tuhume-tuhume 11 da aka gabatar a kan waɗanda aka samu da hannu a laifin.

Source: Original
Hukuncin da kotun Edo ta yanke
Sunayen mutanen da aka samu da aikata laifuffukan su ne Marvelous Isaac, mai shekara 32; Wisdom Michael, mai shekara 36; Rufus Michael, mai shekara 30; da Gift Raphael, mai shekara 27.
Babbar Kotun ta same su huɗu da laifuffukan da ke cikin tuhume-tuhumen, sannan ta yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaoto.
Gwamnan Edo ya dauki zafi
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan Edo, Sanata Monday Okpebholo ya nuna damuwa game da karuwar laifuffukan masu garkuwa da mutane a jihar.
Gwamna ya bayyana cewa za a aiwatar da hukuncin kisa a fili kan waɗanda aka samu da laifin garkuwa da mutane da ‘yan daba bayan an yanke musu hukunci a kotu.
Ya ce gwamnatinsa za ta kafa kotu ta musamman domin shari’ar masu laifi cikin gaggawa, sannan kuma a aiwatar da hukuncin kisa a fili domin zama izina ga wasu.
Asali: Legit.ng
