Talakawa Sun Fasa Rumbun Ajiyar Abinci, Sun Kwashi Shinkafa da Taliya
- Wasu fusatattun mazauna Osogbo a jihar Osun sun kutsa cikin rumbun ajiyar kaya tare da kwashe kayan abinci bayan masu wani shirin sayar da abinci mai rahusa sun ɓace
- Lamarin ya faru ne a ofishin Global Food Initiative da ke yankin Odi-Olowo, Osogbo, inda mutane da dama suka ajiye kuɗi domin sayen abinci a farashin da bai kai na kasuwa ba
- Masu sayen kayan sun ce sun taru a ofishin ne bayan sun kasa samun masu gudanar da shirin, yayin da daga baya wasu suka buɗe rumbun ajiyar suka fara kwashe abinci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Osogbo – Wasu mazauna Osogbo a jihar Osun sun mamaye ofishin Global Food Initiative da ke Odi-Olowo tare da kwashe kayan abinci daga rumbun ajiyar ƙungiyar bayan masu gudanar da shirin sun ɓace.
Lamarin ya biyo bayan tashin hankalin da ya fara kunno kai ranar Litinin, lokacin da mutanen da suka biya kuɗi domin sayen kayan abinci masu rahusa suka taru suna jiran masu gudanar da shirin.

Source: Twitter
An damfari jama'a a Osun
Wata mata mai suna Mistura ta shaida wa Punch cewa ta biya N300,000 ranar Laraba domin sayen buhunan shinkafa 11, inda ake sayar da kowanne N27,000.
Ta ce ana ba su kayan ne mako guda bayan biyan kuɗi, inda ta bayyana cewa buhunan shinkafar 11 da ta biya N300,000 a kansu za su kai N605,000 idan ta saye su a farashin kasuwa na N55,000 kowanne.
Mistura ta ce ta je ofishin ranar Litinin ta tarar da jama’a da dama suna jiran a mika masu kayan su, amma masu gudanar da shirin ba su bayyana ba.
Ta ce kuɗin da ta biya na kayan abincin za a yi amfani da su ne wajen bikin auren ’yar kishiyarta.
Jama’a sun ki barin wurin
A ranar Talata, mutanen da suka biya kuɗin kayan abinci sun sake taruwa a ofishin domin jiran dawowar masu gudanar da shirin.

Kara karanta wannan
Karshen alewa: Kotu ta kama mutum 4 da laifin garkuwa da mutane, ta yanke masu hukunci
Mai gidan da ofishin yake ya roƙi jama’ar da su yi haƙuri tare da bai wa jami’an tsaro damar gano masu gudanar da shirin da kuma samar da hanyar dawo da kuɗin da aka biya.
Sai dai fusatattun mutanen sun ƙi barin wurin, inda lamarin ya ƙara tsananta.

Source: Original
An yi wasoson kayan abinci
Da misalin ƙarfe 4:00 na yamma ranar Talata, wasu daga cikin mutanen sun tilasta buɗe rumbun ajiyar kayan abincin, inda suka fara kwashe kayayyakin da aka ajiye.
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa daga cikin kayan da aka kwashe akwai buhunan shinkafa, taliya da man gyada.
Rahotanni sun ce waɗanda suka shiga rumbun sun ci gaba da kwashe kayan duk da ruwan sama mai ƙarfi, yayin da ’yan sanda kalilan da ke wurin suka yi ƙoƙarin shawo kan lamarin.
A lokacin da rahoton ya fito, ana ci gaba da kwashe kayan, yayin da jami’an tsaro ke harba hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa jama’ar.
Ga bidiyon da aka kwashi abincin da Osun Defender ya wallafa a X:
An kashe mai shayi a Yola
A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar ’yan sandan Adamawa ta fara bincike kan mutuwar Muhammad Auwal Idris, wani matashin mai sayar da shayi a Nassarawo Borehole da ke Jimeta.
An ce ɗan uwan mamacin, Aliyu Idris, ya kai rahoton lamarin hedikwatar ’yan sanda ta Doubeli a ranar 28 ga Satumba, inda ya ce wasu mutane huɗu sun kai wa ƙaninsa hari.
Bayan samun rahoton, jami’an ’yan sanda sun je wurin inda suka tarar da Muhammad Auwal kwance, suka garzaya da shi asibiti, amma likita ya tabbatar da rasuwarsa.
Asali: Legit.ng

