Tsohon Ɗan Wasan Super Eagles Ya Koma Tafiyar Tinubu Gadan Gadan, Ya Shirya Gasa

Tsohon Ɗan Wasan Super Eagles Ya Koma Tafiyar Tinubu Gadan Gadan, Ya Shirya Gasa

  • Tsohon ɗan wasan Super Eagles ya sanar da shirya gasar ƙwallon matasa domin tallafa wa kamfen ɗin Shugaba Bola Tinubu a 2027
  • Ya ce za a gudanar da gasar mai suna Renewed Hope a watan Nuwamba, tare da halartar ƙungiyoyi daga shiyyoyin siyasa shida na Najeriya
  • Tsohon ɗan wasan Inter Milan ya ce zai ɗauki nauyin gasar da kansa, domin tallafa wa matasa da kuma ƙoƙarin Shugaba Tinubu wajen tafiyar da ƙasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ikeja, Lagos - Tsohon ɗan wasan Super Eagles, Obafemi Martins, ya sanar da shirin shirya gangamin kamfen ga Bola Tinubu.

Martins ya shirya gasar ƙwallon ƙafa ta matasa domin tallafa wa kamfen ɗin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.

Tsohon dan wasan Super Eagles zai tallafa Tinubu
Tsohon dan wasan Super Eagles, Obafemi Martins a cikin fili. Hoto: Super Eagles.
Source: Getty Images

Martins ya bayyana hakan ne yayin wata hira da TVC ranar Alhamis, inda ya ce za a gudanar da gasar mai suna “Renewed Hope Tournament” a watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

2027: Sanata Yari ya yanke hukunci kan wanda ya cancanta tsakanin Tinubu, Atiku da Peter Obi

Yadda Martins ya tsara gasar saboda Tinubu

A cewar tsohon ɗan wasan Inter Milan da Newcastle United, gasar za ta ƙunshi ƙungiyoyi daga shiyyoyin kasa shida, tare da ƙarin ƙungiyoyi da za su halarta.

Ya ce gasar za ta kasance ne domin tallafa wa kamfen ɗin Tinubu, tare da samar da damammaki ga matasan Najeriya.

Ya ce manufar shirin ba wai tallafa wa kamfen ɗin Tinubu kaɗai ba ce, har ma da samar da damammaki ga matasan Najeriya.

Martins ya ce:

“Akwai wata gasa da nake shirya wa Mai Girma Bola Ahmed Tinubu domin kamfen ɗinsa, gasar matasa ta sabunta fata, kuma ina yin ta da shiyyoyin siyasa, waɗanda shida ne, sannan ina ƙara wasu ƙungiyoyi biyu zuwa uku.
“Ina ganin ina farin cikin yi wa shugaban ƙasa hakan saboda dukkanin ƙoƙarin da yake yi. Kuma wannan ba don shugaban ƙasa kaɗai ba ne, har ma ga ’yan Najeriya da matasan Najeriya, da yadda za mu taimaka musu.”

Kara karanta wannan

Ba boye boye kungiyar malaman addini ta bayyaana dalilin goyon bayan Tinubu a 2027

Obafemi Martins ya dawo tafiyar Tinubu
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Dada Olusegun.
Source: Facebook

Yaushe za a fara gasar saboda Tinubu?

Martins ya bayyana cewa shi da kansa zai ɗauki nauyin gasar, inda ya tabbatar da cewa za a gudanar da ita a watan Nuwamba.

Da aka tambaye shi ko shi da kansa zai ɗauki nauyin gasar, ya ce:

“Eh, zan yi ta a watan Nuwamba.”

Sanarwar ta zo ne makonni biyu kacal bayan Martins ya nuna goyon bayansa ga ɗan Tinubu, Seyi Tinubu, domin ya zama shugaban Hukumar Kwallon Ƙafa ta Najeriya (NFF) nan gaba.

Yayin wata tattaunawa a shirin Mikel Obi, Martins ya bayyana Seyi a matsayin matashi mai fahimtar abubuwan da ’yan Najeriya ke buƙata.

Martins ya ce:

“Ina ganin Seyi Tinubu zai iya zama shugaban NFF. Matashi ne kuma ya fahimci abin da ’yan Najeriya ke so. Ba shugaban ƙasa ba ne tukuna, amma yana ƙoƙari.”

Sabon shirin Martins ya ƙara nuna irin ayyukan da yake yi a harkar ƙwallon matasa, tare da goyon bayansa ga gwamnatin Tinubu gabanin babban zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Dan takara ya yi alkawarin samar da lantarki a kowane gida cikin watanni 11 a Najeriya

2027: Sanata Yari ya koɗa Tinubu

Mun ba ku labarin cewa Abdulaziz Yari ya ce babu wani ɗan takarar shugaban ƙasa ya kama kafar Shugaba Bola Tinubuwajen cancanta, ƙwarewa da nagarta.

Sanatan ya nemi ’yan Jam’iyyar APC su yi aiki tukuru domin ganin Tinubu ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Yari ya kuma bukaci magoya bayan APC su yi wa Tinubu da Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, addu’ar samun nasara a zaɓensu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.