Takarar ‘Dan Gwamna El-Rufai a 2023 ta yi waje da ‘Dan Majalisan Kaduna daga Jam'iyyar APC

Takarar ‘Dan Gwamna El-Rufai a 2023 ta yi waje da ‘Dan Majalisan Kaduna daga Jam'iyyar APC

  • Kwanaki Hon. Samaila Suleiman ya bar APC zuwa PDP da sunan jam’iyya mai mulki na fama da rikici
  • Gaskiyar abin da ya faru shi ne ‘Dan majalisar na Kaduna ta Arewa ya hango ba zai samu tikiti APC ba ne
  • Alamu masu karfi sun nuna Bello El-Rufai ne wanda jam'iyyar APC za ta ba takara a yankin a zaben 2023

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - A watan Maris na 2022 ne aka ji Hon. Samaila Suleiman ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki, a karshe ta tabbata ya sauya-shekarsa zuwa PDP.

Samaila Suleiman ya fake da rikicin cikin gidan APC a matsayin dalilin sauya-shekarsa. Daily Trust ta bayyana cewa ba gaskiyar maganar kenan ba.

Suleiman mai wakiltar Kaduna ta Arewa a majalisar wakilan tarayya ya bar APC ne saboda ya lura Bello El-Rufai yana harin kujerarsa a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Mai neman takara ya samu tikitin PDP yayin da yake hannun masu garkuwa da mutane

Bello El-Rufai shi ne babban 'dan Mai girma gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai. Matashin ya dade da sha’awar siyasa, kamar yadda mahaifinsa ya taba fada.

Shugaban kwamitin na harkoki na musamman a majalisar wakilan tarayya ya hango ba zai samu tikitin 2023 ba, hakan ta sa ya yi maza ya canza gida.

Bello v Sulaiman

Fitar Sulaiman daga APC mai mulki ta bada mamaki, ganin cewa ya fi Bello El-Rufai gogewa a siyasa, amma sai ya ki bari su gwabza zaben tsaida gwani.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

‘Dan Gwamna El-Rufai
Bello El-Rufai Hoto: @bello.elrufai
Asali: Facebook

Hon. Sulaiman ya rike shugaban karamar hukuma, daga nan aka zabe shi ‘dan majalisar tarayya a 2015. Shi ma mahaifinsa, babban ‘dan siyasa ne a Kaduna.

A gefe guda, Bello El-Rufai shi ne babban hadiman Sanatan Kaduna ta tsakiya, Uba Sani. Kafin tafiyarsa a majalisa a 2019, ya yi aiki da manyan kamfanoni.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Babban abin da ya sa har gobe Shugaba Buhari yake kaunar Amaechi - El-Rufai

Za a ba yaron Gwamna tuta

Jaridar ta ce ‘dan majalisar ya zabi ya nemi takara a jam’iyyar PDP ne domin manyan APC a Kaduna sun yi wa ‘dan gwamnan alkawarin zai samun tikiti.

Sakataren yada labaran APC na jihar Kaduna, Salisu Tanko Wusonu, ya karyata wannan magana, ya ce jam’iyya ba tayi wa kowa alkawarin wani tikiti a zabe ba.

Suleiman ya samu tikitin PDP

Labarin da mu ke samu shi ne Suleiman ya samu tikitin PDP da kuri’u 20 bayan ya doke Shehu Usman ABG da kuma Baffa Namadi Sambo masu kuri’u 14 da 2.

Suleiman ya yi nasara a zaben fitar da gwanin da aka shirya a ranar Lahadi. Idan ta tabbata, zai yi takarar majalisa a karo na uku kenan a jere a shekara mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel