Shettima Ya Tafi Muhimmin Taron da za a Yi da Iran, Rasha da Wasu Kasashe

Shettima Ya Tafi Muhimmin Taron da za a Yi da Iran, Rasha da Wasu Kasashe

  • Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya bar Abuja zuwa Indiya domin wakiltar Shugaba Bola Tinubu a taron shugabannin BRICS na 18
  • Taron zai mayar da hankali kan ƙarfafa haɗin gwiwa a fannin kasuwanci, zuba jari, makamashi, noma, ma’adinai, fasaha da ƙirƙire-ƙirƙire
  • Nigeria na amfani da matsayinta na abokiyar hulɗar BRICS wajen neman damammaki na tattalin arziki da ƙarfafa dangantaka da manyan ƙasashe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya bar Abuja zuwa birnin New Delhi na Indiya, domin wakiltar Shugaba Bola Tinubu a taron shugabannin ƙasashen BRICS na 18.

Taron zai gudana ne a ƙarshen wannan mako, yayin da shugabannin ƙasashe da manyan jami’ai daga sassa daban-daban na duniya za su taru a New Delhi.

Kara karanta wannan

'Abin da ya sa nake so ƴan Najeriya su sake zaɓen Tinubu': Oluremi

Kashim Shettima a jirgi
Lokacin da Kashim Shettima ke fita daga jirgi. Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Hadimin mataimakin shugaban kasa, Stanley Nkwocha ne ya fitar da sanarwa game da tafiyar Shettima a wani sako da ya wallafa a X.

Abubuwan da za a tattauna a taron

BRICS wata ƙungiya ce ta ƙasashe 11 masu tasowa da ƙasashe masu karfin tattalin arziƙi, wadda ke ƙara faɗaɗa haɗin gwiwa a tsakanin mambobinta.

Ƙasar Indiya ce ke jagorantar BRICS a shekarar 2026, inda taken shugabancinta shi ne gina tattalin arziki, ƙirƙire-ƙirƙire, haɗin gwiwa da ɗorewa.

The Nation ta wallafa cewa ana sa ran taron zai tattauna batutuwan siyasa da tsaro, haɗin gwiwar tattalin arziki da kuɗi, da kuma hulɗar al’adu da jama’a.

Kasashen BRICS sun hada da China, Egypt, Ethiopia, India, Indonesia, Iran, Russia, Saudi Arabia, Afrika ta Kudu, da UAE.

Me Shettima zai yi a can?

Yayin zamansa a New Delhi, Shettima zai shiga zaman shugabannin ƙasashen BRICS da na ƙasashen abokiyar hulɗa, tare da halartar tarukan manyan jami’ai.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya ware gwamna a Arewa ya kwararo masa yabo

Zaman zai mayar da hankali kan bunƙasar tattalin arzikin duniya, haɗin gwiwar ƙasashe da kuma abubuwan da za su taimaka wajen samun ci gaba mai ɗorewa.

Taron BRICS na 2025
Taron BRICS na 2025 a Brazil. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ana kuma sa ran Mataimakin Shugaban Ƙasar zai gana da wasu shugabanni da manyan jami’an gwamnatocin ƙasashen da za su halarci taron.

Tattaunawar za ta mayar da hankali kan hanyoyin ƙara haɗin gwiwar tattalin arziki da diflomasiyya tsakanin Nigeria da sauran ƙasashen.

Nigeria ta zama ƙasar abokiyar hulɗar BRICS tun watan Janairun 2025, kuma tana amfani da dandalin wajen ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasashen Kudancin Duniya.

Shettima ya yabi NELFUN

A wani labarin, mun ruwaito cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya bayyana asusun NELFUND, a matsayin wani babban shiri da ke taimaka wa ɗalibai.

Shettima ya ce shirin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta kafa ya zama wata hanya ta rage bambancin da ke tsakanin masu hali da marasa hali wajen samun ilimin manyan makarantu.

Ya ce NELFUND na biyan kuɗin makaranta tare da bayar da tallafin kula da kai na wata-wata, lamarin da ya taimaka wajen rage matsalolin kuɗi da ke hana wasu ɗalibai ci gaba da karatu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng