Peter Obi Ya Shiga Maganar Kashe Dan Shagamu a Kano, Ya Yi Kira ga Hukuma
- Ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi, ya yi Allah-wadai da kisan mashahurin mai sharhi a kafafen sada zumunta, Ibrahim Khalil Dan Shagamu
- Obi ya buƙaci gwamnatin Kano da hukumomin tsaro su gudanar da cikakken bincike domin gano waɗanda suka aikata kisan tare da hukunta su
- ’Yan sanda a Kano sun ce sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan Dan Shagamu, yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Tsohon gwamnan jihar Anambra kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya buƙaci a gudanar da cikakken bincike kan kisan Ibrahim Khalil Dan Shagamu.
Rahotanni sun nuna cewa wasu mutane ne suka shiga har gida suka kashe mai sharhi kan lamuran yau da kullum din a Kano.

Source: Facebook
Obi ya yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Juma’a, inda ya yi Allah-wadai da kisan.
Obi ya ce a hukunta masu laifi
Peter Obi ya buƙaci gwamnatin jihar Kano da hukumomin tsaro da abin ya shafa su gudanar da bincike mai zurfi, gaskiya da adalci kan lamarin.
Ya kuma nemi a gurfanar da duk waɗanda aka samu da hannu a kisan tare da hukunta su bisa doka.
Obi ya ce:
“Na yi matuƙar baƙin ciki kan kisan mai sharhi a kafafen sada zumunta, Ibrahim Khalil Dan Shagamu, a gidansa da ke Kano.
“Babu rashin jituwa, suka ko wata takaddama tsakanin maƙwabta da za ta iya zama hujjar kashe mutum.
“Ba za a bar masu bayyana ra’ayoyinsu ko waɗanda ke da ra’ayoyi daban-daban su rayu cikin tsoro ba.”
Yadda aka kashe Dan Shagamu
Dan Shagamu ya rasa ransa ne a gidansa da ke unguwar Gaida, a ƙaramar hukumar Kumbotso ta jihar Kano, a daren Litinin.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta ce an kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a lamarin.
A cewar ’yan sandan, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:30 na dare bayan kwamandan kungiyar ’yan sa-kai na Gaida ya kai rahoton lamarin.
Jami’an ’yan sanda daga sashen Kumbotso sun isa wurin tare da kai Dan Shagamu zuwa Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed da ke Kano, inda likita ya tabbatar da rasuwarsa.

Source: Original
’Yan sanda na bincike
Rundunar ta ce mutanen da ake zargin suna hannunta kuma ana yi musu tambayoyi, yayin da ake gudanar da binciken domin gano ainihin yadda lamarin ya faru da kuma dalilin kai harin.
Punch ta wallafa cewa Obi ya kuma jaddada cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba ’yan ƙasa ’yancin faɗar albarkacin baki.
Ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan Dan Shagamu, abokansa, abokan aikinsa da mabiyansa, tare da addu’ar Allah ya jiƙansa.
Maganar da Kwankwaso ya yi
A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya buƙaci a gudanar da bincike kan kisan Ibrahim Khalil Dan Shagamu.
Kwankwaso ya bayyana kisan a matsayin wani mummunan hari, inda ya buƙaci gwamnatin Gwamna Abba Yusuf ta kafa kwamitin.
Ya kuma ce idan gwamnatin da ke kan mulki ta gaza ɗaukar matakin da ya dace, gwamnatin NDC za ta sake buɗe binciken lamarin idan ta samu nasara a zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng


