Da Gaske Peter Obi Ya Ce Yarbawa Musulmai ba Sa Yin Musulunci na Gaskiya?
- An yada wani rubutu mai cewa Peter Obi ya bayyana cewa Yarbawa musulmai ba sa yin Musulunci na gaskiya
- Hoton ya danganta kalaman da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) a wata hira da aka yi da shi
- An gudanar binciken kan bidiyon hirar domin gano hakikanin ko dan takarar shugaban kasar ya yi wadannan kalaman
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Wasu masu amfani da kafafen sada zumunta sun yada wani hoto dauke da Peter Obi da wasu kalamai da ake cewa ya yi kan Yarbawa musulmo.
A cikin hoton an danganta Peter Obi wanda yake takarar shugaban kasa na Nigeria Democratic Congress (NDC), da wani furuci cewa “Yarbawa musulmai ba sa yin Musulunci na gaskiya”

Source: Facebook
Hoton da aka yi amfani da shi a sanarwar ya fito ne daga wata hira da Peter Obi ya yi da Arise Tv.
An yada maganganu kan Peter Obi
Sanarwar ta ce:
“Yarbawa Musulmai ba sa yin Musulunci na gaskiya. Musulunci na gaskiya ana yin sa ne kawai a Arewa, shi ya sa ya kamata shugaban kasa ya yi Sallah a Sokoto ko Kano.”
Wannan hoton ya nuna cewa Obi ne ya furta kalaman a yayin hirarsa da tashar wanda aka sanya a ranar Alhamis, 10 ga watan Satumban 2026.
Wani mai amfani da X mai suna @Sistaliano ya wallafa hoton tare da cewa:
“Wannan cin mutunci ne ga Yarbawa, musamman Musulmi. Ya kamata wani ya kira wannan wawan ya ja masa kunne. Saboda Allah mene ne wannan?” An adana kwafin sakon.
Sakon ya samu fiye da sake wallafawa 130, sharhi 250 da kuma likes 250.
Wani mai amfani da X, @YemmyAj, shi ma ya wallafa hoton tare da cewa:
“Ka ba Peter Obi makirufo, zai yi wa kansa kamfen ne.”
An kuma wallafa hoton a wasu shafuka daban-daban.
Hoton ya bayyana a kafafen sada zumunta ne bayan tashar watsa wata hira da Obi wadda ba ta kai mintuna 50 ba.
An binciki maganar Peter Obi
The CableCheck ta kalli cikakken bidiyon hirar Obi da tashar wadda aka wallafa a YouTube.
A cikin hirar baki daya, dan takarar shugaban kasa na NDC bai ambaci kalaman da aka yada a kafafen sada zumunta ba.
Abin da Obi ya fada dangane da Musulunci shi ne cewa, idan aka zabe shi shugaban kasa, zai yi hutun Sallah tare da Sarkin Musulmi na Sokoto.
Obi ya soki Shugaba Bola Tinubu kan yadda yake yin hutun Sallah a Legas, inda ya ce idan aka zabe shi zai yi amfani da lokacin wajen hada kan ’yan Najeriya a Arewa.
“Sallah da komai, shi (Tinubu) yana yin sa a Legas. Musulmi ne. Zan je Sokoto in yi Sallah tare da Sarkin Musulmi, mu hada kowa wuri guda sannan mu tattauna makomar kasa. Zan je Kano,” in ji Obi.

Kara karanta wannan
Gwamna Abba ya yi magana mai tsauri kan kisan fitaccen mai sharhi kan siyasa a Kano
Abin da bincike ya gano
Binciken da aka gudanar ya nuna ikirarin cewa Peter Obi ya ce Yarbawa Musulmai ba sa yin Musulunci na gaskiya karya ce.
Saboda haka babu kamshin gaskiya a cikin kalaman da ake dangantawa da tsohon gwamnan na jihar Anambra.

Source: Facebook
Peter Obi ya yi magana kan Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Peter Obi ya ce akwai lokutan da yake ganin ba Shugaba Bola Tinubu ba ne ke da cikakken iko kan gwamnatinsa ba.
Dan takarar na NDC ya ce ya kamata Tinubu da kansa ya riƙa yi wa ’yan Najeriya bayani kan batutuwan da suka shafi ƙasar, maimakon barin mataimakansa su riƙa magana a madadinsa.
Asali: Legit.ng

