Ba sani ba sabo: Dan majalisar tarayyar APC daga Kaduna ya sha tambayoyi a EFCC
Dan majalisar wakilai dake wakiltar karamar hukumar Kaduna ta Arewa a majalisar, Samaila Suleman, ya kwashe sama da awanni hudu yana amsa tambayoyi a hedikwatar Hukumar EFCC a Kaduna, sakamakon wasu tuhume tuhume da aka yi masa akan badakalar wasu kudade.
Samaila Suleman wanda dan jam'iyyar APC ne tun da fari EFCC ta kai samame gidanshi dake Kaduna sakamakon korafe-korafe da suka hada da zamba cikin aminci da kuma sama da fadi da wasu makudan kudade da suka samu daga wasu mutane.

Asali: Facebook
KU KARANTA: Tsaffin gwamnoni 2 za su san makomar su yau a kotu
Legit.ng Hausa ta samu cewa Hon. Samaila Suleman ya bayyanawa 'yan jarida cewar yazo hukumar ne domin bincike akan cewar ana nemanshi kuma anje gidan shi ba a same shi ba sannan kuma ya yadda ya tabbatar cewa babu wata matsala tsakanin shi da EFCC din.
A wani labarin kuma, hukumar gwamnatin tarayya dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa tu'annati watau Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) ta sanar da samun nasarar cafke wasu hatsabiban dalibai da suka kware wajen zamba cikin aminci da damfara a kafafen sadarwar zamani da yanar gizo.
Daliban wadan da suka kai akalla 34 an kama su ne a wani gida mai lamba 21 dake a kan titin Sawmill, unguwar Awa-Ijebu, jihar Ogun kuma dukkan su basu wuce shekaru 19 zuwa 37 ba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng