Trump Ya Watsa wa Saudiyya Kasa a Ido, Ya Ki Amince wa da Rokon Yarima
- Yariman Saudiyya Mohammed bin Salman ya kira Shugaba Trump sau biyu yana neman Amurka ta kai hare-hare kan mayakan Houthi
- Trump ya ƙi amincewa da buƙatar, yayin da jami’an Amurka suka ce gwamnatin Amurka ba ta shirin shiga yaƙi kai tsaye da Houthi a yanzu
- Ƙwace wani muhimmin birnin gabar tekun Yemen da Houthis suka yi ya sa farashin man fetur ya tashi saboda barazanar mashigar Bab al-Mandab
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Riyadh, Saudiyya - Yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman (MBS), ya kira Shugaban Amurka Donald Trump sau biyu ranar Alhamis, 10 ga watan Satumban 2026.
Mohammed bin Salman ya roƙi Shugaba Trump da ya umarci sojojin Amurka su kai hare-hare kan mayakan Houthi.

Source: Getty Images
Jami’an Amurka biyu ne suka bayyana hakan ga tashar Axios, yayin da kungiyar da Iran ke mara wa baya ke ƙara matsowa kusa da mashigar Bab al-Mandab, wadda ke da matuƙar muhimmanci ga kasuwancin duniya.

Kara karanta wannan
Shugaban Amurka ya 'tsorata', ya fara laluben lokacin dakatar da yaki da ƙasar musulunci ta Iran
Sai dai Trump ya ƙi amincewa da buƙatar, yayin da jami’an Amurka suka jaddada cewa a halin yanzu gwamnatin ba ta da shirin shiga tsakani kai tsaye a yaƙin da mayakan Houthi.
Farashin man fetur ya tashi
Farashin man fetur a kasuwannin duniya ya yi tashin gwauron zabi ranar Alhamis, bayan da mayakan Houthi suka ƙwace wani muhimmin birnin gabar tekun Yemen.
Ƙwace birnin ya sa kungiyar ta ƙara matsowa kusa da mashigar Bab al-Mandab, wadda hanya ce mai matuƙar muhimmanci ga jigilar kayayyaki a duniya da kuma fitar da man Saudiyya zuwa kasuwannin duniya.
Iran ta riga ta kawo cikas ga zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigar Hormuz. Idan Houthis suka samu cikakken iko kan Bab al-Mandab, hakan na iya bai wa Tehran wata muhimmiyar hanyar matsa wa Amurka da kawayenta na Gulf.
Amurka na ƙara tallafa wa Saudiyya
Amurka na nuna damuwa kan yadda rikicin Yemen ke ƙara kamari cikin sauri, inda take ƙara tallafa wa Saudiyya amma tana ƙoƙarin kauce wa shiga yaƙin kai tsaye.
Admiral Brad Cooper, kwamandan Rundunar Sojin Amurka a Gabas ta Tsakiya, ya je Saudiyya ranar Alhamis domin gudanar da tarukan gaggawa na daidaita matakan da za a ɗauka, a cewar majiyoyi biyu da ke da masaniya kan lamarin.
Ofishin jakadancin Saudiyya da ke Washington da Fadar White House sun ƙi yin tsokaci kan lamarin.
Rikicin Saudiyya da Houthis ya sake kunno kai
Rikicin tsakanin Saudiyya da Houthis ya sake barkewa ne a watan Yuli, bayan da Riyadh ta hana wani jirgin saman Iran ɗauke da manyan jami’an Houthi sauka a birnin Sanaa.
Jirgin na ɗauke ne da jami’an kungiyar da suka dawo daga jana’izar tsohon Jagoran Addinin Iran, Ali Khamenei.
MBS ya nemi Trump ya ba shi goyon bayan siyasa domin kai hari kan filin jirgin saman Sanaa, amma ya bayyana cewa Saudiyya ba ta buƙatar taimakon sojin Amurka.
Trump ya ba shi goyon bayansa kan harin wanda ya hana jirgin saman sauka a filin jirgin.
Mayakan Houthis sun mayar da martani
Daga bisani, mayakan Houthi suka mayar da martani ta hanyar kai hare-hare kan jiragen ruwan Saudiyya da ke ɗauke da mai a Bahar Maliya.
Hakan ya jefa babbar barazana ga muhimmiyar hanyar da Saudiyya ke amfani da ita wajen fitar da man fetur, sannan kungiyar ta faɗaɗa hare-harenta zuwa cibiyoyin makamashi na ƙasar.
Saudiyya da kawayenta na Yemen sun mayar da martani ta hanyar kai hare-haren sama da kuma hare-haren ƙasa kan wuraren da Houthi ke iko da su.
MBS ya sake kiran Trump
Ranar Alhamis, yayin da dakarun Houthi ke matsowa kusa da birnin Mokha na gabar tekun Yemen, sannan dakarun Yemen da Saudiyya ke marawa baya suka ja da baya, MBS ya kira Trump domin sanar da shi yadda lamarin ke ƙara taɓarɓarewa.
Bayan wasu sa’o’i, MBS ya sake kiran Trump, inda ya roƙe shi da ya ba da umarnin kai hare-haren Amurka kan Houthi. Trump ya ƙi amincewa da buƙatar.
Sai dai wani jami’in Amurka ya ce gwamnatin za ta samar wa Saudiyya bayanan sirri da suka shafi Houthi da kuma bayanan wuraren da za a iya kai wa hari.

Source: Getty Images
Saudiyya ta kai hare-hare Yemen
A wani labarin kuma, kun ji cewa jiragen yaƙin Saudiyya sun kai hare-haren sama kusan 40 kan wasu yankunan a Taiz, lardin Hodeidah, Al-Jawf da Marib da ke kasar Yemen.
Jiragen yakin na Saudiyya sun kai hare-hare a gundumomin As-Salif da At-Tuhayta, da kuma tsibirin Kamaran da ke Yemen.
Asali: Legit.ng

