NAHCON Ta Jero Kamfanonin Jiragen Sama 5 da Za Su Yi Jigilar Mahajjatan Najeriya a Hajjin 2027
- Hukumar alhazan Najeriya (NAHCON) ta amince da kamfanonin jiragen sama 5 domin jigilar mahajjatan Najeriya a Hajjin 2027
- Wannan dai na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen aikin Hajjin badi, wanda NAHCON ke sa ran sauke nauyinta da wuri
- An ce kamfanonin za su cika ka’idojin tsaro da na hukumomin zirga-zirgar jiragen sama na Najeriya da Saudiyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta amince da kamfanonin jiragen sama guda biyar domin gudanar da jigilar mahajjatan Najeriya a aikin Hajjin 2027.
NAHCON ta tabbatar da hakan ne a wata takardar sanarwa da hukumar ta fitar a Abuja ranar Alhamis, 13 ga watan Agustan 2026.

Source: Facebook
NAHCON ta tantance kamfanonin sosai
NAHCON ta ce zabin kamfanonin ya biyo bayan wasu tsauraran matakin tantancewa da tantance kwarewa da kwamitin tantance harkokin jiragen sama ya gudanar a kansu.
Ta ce an yi tantancewar ne bisa ka’idojin tsaro, karfin gudanar da aiki da kuma yanayin karfin kudi na kamfanonin.
Hukumar NAHCON ta ce:
“Gwamnati ta amince da shigar da kamfanonin jiragen sama guda biyar cikin aikin Hajjin 2027.”
Sai dai ta ce amincewar tana karkashin sanya hannu kan yarjejeniyar jigilar mahajjata tsakanin kamfanonin da NAHCON, da kuma cika sharuddan Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Saudiyya (GACA).
Sunayen kamfaninin jirage 5
Kamfanonin da hukumar NAHCON ta amince su yi jigilar maniyyatan Najeriya a aikin Hajji mai zuwa, su ne:
- Air Peace Limited
- Flynas
- Max Air Limited
- Saudi Air
- UMZA Aviation Services Limited
Hukumar ta ce za a tsara rabon mahajjata da jadawalin jigilar su tare da hukumomin jin dadin mahajjata na jihohi da kuma kamfanonin jiragen saman da abin ya shafa.
An sanya sharuddan jigilar mahajjata
NAHCON ta ce dukkan kamfanonin da aka amince da su dole ne su gudanar da ayyukansu bisa ka’idojin Hajjin 2027, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan
Gwamnan APC ya ƙaƙaba harajin N150m kan Bola Tinubu da wasu yan takara a zaben 2027
Daga cikin sharuddan akwai bayar da tikitin jirgi da ke hade da bayanan mahajjata na Nusuk-Masar, tare da bin dukkan ka’idojin tsaro na zirga-zirgar jiragen sama.

Source: Facebook
Hukumar ta kuma ce an kayyade nauyin kayan da kowane mahajjaci zai iya dauka, wanda ya hada da jaka guda mai nauyin kilo 32 da kuma kayan hannu guda mai nauyin kilo 8.
Hukumar ta yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su hada kai da kamfanonin da aka amince da su domin tabbatar da jigilar mahajjatan Najeriya cikin sauki, tsaro da kwanciyar hankali a lokacin aikin Hajjin 2027.
Maniyyata za su fara ajiye N5m
A wani rahoton an ji cewa Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta buƙaci masu niyyar gudanar da aikin Hajjin 2027 su fara ajiye kuɗi har Naira miliyan 5.
A cikin wata sanarwa, hukumar ta ce fara biyan kuɗin tun da wuri zai ba maniyyata damar tabbatar da samun gurbi da rage musu nauyin biyan kuɗin Hajji lokaci guda.
Ta buƙaci masu sha'awar zuwa Hajji su fara tara kuɗinsu ta hannun Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta jiharsu ko kuma bankunan da akaNamince da su
Asali: Legit.ng
