Ana Shirin Binciken Adeyemi, Shugaban PFIPC na Bogi Ya Roki Alfarmar Majalisa

Ana Shirin Binciken Adeyemi, Shugaban PFIPC na Bogi Ya Roki Alfarmar Majalisa

  • Kwamitin Majalisar Wakilai da ke binciken badakalar PFIPC bai riga ya yanke shawarar wurin da zai yi wa Adeniyi Adeyemi tambayoyi ba
  • Sai dai majalisar ta tabbatar da cewa za a titsiye Adeyemi bayan an gano cewa ya kada hukumar bogi tare da bayyana kansa a matsayin shugabanta
  • Adeyemi ya dage kan cewa lallai a duba wasu manyan bukatu biyu da ya ke bukata a lokacin da 'yan majalisar wakilai za su yi masa tambayoyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Kwamitin musamman na Majalisar Wakilai da ke binciken rikicin PFIPC ya tabbatar da cewa za a titsiye Adeniyi Adeyemi a kan yadda ya kafa hukumar.

Sai dadi duk da wannan tabbaci, har yanzu bai yanke shawarar inda zai yi wa Adeniyi Adeyemi tambayoyi a kan yadda ya shammaci yan Najeriya ba.

Kara karanta wannan

Yadda za ku duba sunayen waɗanda hukumar Kwastam ta ɗauka aiki a 2026

Ana shirin titsiye Adeyemi a majalisar Najeriya
Shugaban PFIPC, hukumar bogi a Najeriya Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

A labarin da ya kebanta ga jaridar Punch, wata majiya ta ce Adeyemi ya dage cewa lauyoyinsa da ’yan jarida dole su kasance a wurin kafin ya amince da amsa tambayoyin kwamitin Majalisar.

PFIPC: Bukatar Adeyemi ga majalisa

Kwamitin wanda dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar tarayya ta Kanke/Kanam/Pankshin a Jihar Plateau, Yusuf Gagdi, ke jagoranta, na binciken yadda PFIPC ta samu ofishin gwamnati a sakariyar Abuja.

Haka kuma ana binciken yadda hukumar ta samy sama da N1.32bn a cikin kasafin kudin shekarar 2026, duk da zargin cewa hukumar ba ta da wani tushe na doka.

Har yanzu ba a saka lokacin titsiye Adeyemi ba
Dan majalisar Plateau, Yusuf Gagdi Hoto: Rt. Hon Yusuf Adamu Gagdi, PhD, OON
Source: Facebook

Binciken ya jawo hankalin jama'a sosai sakamakon zargin cewa majalisar ta gudanar da ayyukanta a cikin tsarin gwamnati duk da cewa ba ta da cikakkiyar amincewar doka.

Hakan ya haifar da damuwa kan yiwuwar samun kura-kurai wajen kula da kudaden gwamnati da kuma sa ido kan hukumomin gwamnati.

Shugaban PFIPC na bogi zai je majalisa

Kara karanta wannan

Kano za ta karbi manyan baki, akwai babban taro a kan miyagun kwayoyi

Ana sa ran Adeyemi, wanda ke hannun ’yan sanda sakamakon rikicin da ya shafi majalisar, zai bayyana a gaban kwamitin a wannan makon, bayan da wasu manyan jami’an gwamnati suka gabatar da shaidunsu.

Majiyar, wadda ta nemi a sakaya sunanta saboda ba a ba ta izinin tattaunawa da kafafen yada labarai kan ayyukan kwamitin ba, ta tabbatar da hakan.

Da aka tambaye ta ko kwamitin ya riga ya zabi wurin da Adeyemi zai bayyana, majiyar ta amsa da cewa har yanzu ba a yanke shawara ba.

Wannan ci gaban ya biyo bayan zaman sauraron bayanai da kwamitin ya yi da wasu manyan jami’an gwamnati, ciki har da Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Didi Walson-Jack.

Sauran sun hada da Darakta-Janar na Ofishin Kasafin Kudi na Tarayya, Tanimu Yakubu; Daraktan Ayyukan Banki na Babban Bankin Najeriya (CBN), Hamisu Abdullahi; da wakilan Sufeto-Janar na ’yan sanda.

Tinubu ya karbi rahoton PFIPC

A baya, kun samu rahoton cewa hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta ta ICPC ta mika wa Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu rahoton wucin gadi kan binciken PFIPC ta ake ta magana a kanta.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Yadda shugaban hukumar bogi ta PFIPC ya damfari dan kasuwa N400m

Hukumar ta ce Prince Adeyemi Matthew bai taba samun nadi daga gwamnatin tarayya a hukumance ba duk da cewa ya nada kansa a matsayin shugaban PFIPC tare da nuna kansa a matsayin jami'in gwamnati.

Hukumar ICPC ta bayyana cewa PFIPC ba ta da tushe a doka ko umarnin zartarwa, yayin da takardun nadin da aka yi anfani da su duk na jabun ne, wanda hakan ya wanke gwamanti daga zarge-zargen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng