Asiri Ya Tonu: An Samu Gawar Mace a Coci, Fasto Ya Gudu

Asiri Ya Tonu: An Samu Gawar Mace a Coci, Fasto Ya Gudu

  • Wani malamin addinin Kirista ɗan Najeriya da hukumomin Cameroon ke nema ya buya bayan an gano wata gawa a wani wuri da ke da alaƙa da cocinsa a Yaoundé
  • An gano gawar ne a ranar 19 ga Satumba a ƙarƙashin wani siminti a wani gida da ake alakanta shi da cocin da mutumin ke jagoranta
  • Hukumomin tsaron Cameroon na neman faston, Kedi Samuel Kenechukwu, wanda aka fi sani da Ekedi Samuel, bisa zarge-zargen da suka haɗa da safarar mutane

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Yaoundé – Wani malamin addini ɗan Najeriya da hukumomin Cameroon ke nema ya buya bayan an gano wata gawar da ta rube a wani wuri da ke da alaƙa da cocinsa a Yaoundé.

Rahoto ya nuna cewa jami’an ofishin ’yan sanda na musamman na Nkoabang ne suka gano gawar da misalin ƙarfe 9 na safe a ranar 19 ga Satumba, yayin da suke gudanar da bincike kan Kedi Samuel Kenechukwu, wanda aka fi sani da Ekedi Samuel.

Kara karanta wannan

EFCC na bincikar wasu malaman musulunci da limamai kan laifin kuɗi a Najeriya

Taswirar kasar Kamaru
Taswirar kasar Kamaru. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An gano gawar a coci

Punch ta wallafa cewa Kenechukwu ne wanda ya kafa Mercy of God Ministry, kuma hukumomin tsaron Cameroon na neman sa kan wasu zarge-zarge da suka haɗa da safarar mutane da sace mutane.

Wasu kafafen yaɗa labarai na Cameroon sun ruwaito lamarin, sun bayyana Kenechukwu a matsayin wani dan Najeriya da ke gudanar da aiki a Cameroon tun shekarar 2018.

Rahotanni sun ce gawar da aka gano tana cikin wani yanayi maras kyau, inda aka same ta a ƙarƙashin wani wuri da aka rufe da siminti.

Binciken ya gano wani ɓoyayyen wuri ne bayan wasu mazauna yankin sun lalata sassan gidan, abin da ya bai wa jami’an bincike damar gano wurin da aka ɓoye.

Hukumomi na bincike

A lokacin da rahoton ya fito, jami’an tsaro na jiran izini domin gudanar da ƙarin bincike a wurin don gano ko akwai wasu gawawwaki ko ragowar mutane.

Har yanzu ba a tabbatar da sunan mamaciyar ko kuma abin da ya haddasa mutuwarta ba.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa 7 sun shilla ƙasar Amurka, sun nemo abin da zai amfani 'yan Najeriya

An gano gawar ne kimanin kwanaki 10 bayan jami’an bincike sun gudanar da bincike a wannan gida na Nkoabang a ranar 9 ga Satumba.

A lokacin binciken, jami’an sun gano motoci biyar, ɗaruruwan kilogram na abinci, firij masu aiki da kuma ɗakuna kusan 30 a cikin gidan.

An kuma gano wani rami mai zurfin kusan mita biyu, sai dai ba a tabbatar da dalilin da aka haƙa shi ba a lokacin.

An gano mutane 20

Binciken gidan Nkoabang ya biyo bayan wani samame da aka gudanar a ranar 6 ga Satumba a wani wuri da ake alakanta shi da Mercy of God Ministry da ke Ngousso, Yaoundé.

Rahoton Yen ya ce jami’an tsaro sun gano mutane 20 a cikin wani ɗakin ƙasa, ciki har da mata 10, maza takwas da yara biyu masu shekaru shida da bakwai.

Bayan waɗannan abubuwan da aka gano, hukumomin tsaro sun faɗaɗa bincikensu zuwa wasu wurare da ake zargin suna da alaƙa da cocin.

Paul Biya a kamaru
Shugaban kasar Kamaru, Paul Biya. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Paul Biya ya koma Kamaru

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban Cameroon, Paul Biya, ya koma ƙasarsa bayan shafe sama da wata biyu a ƙasashen waje, lamarin da ya jawo damuwa kan tsawon lokacin da ya yi ba ya cikin ƙasar.

Kara karanta wannan

2027: Matasan Najeriya sun tafi Abuja domin hada Atiku da Obi su kwarfe Tinubu

Rahotanni sun nuna ceewa Paul Biya ya isa birnin Yaoundé ne daga Geneva da ke Switzerland, bayan shafe sama da makonni 10 a wajen ƙasar.

Biya, wanda ya kasance shugaban ƙasa tun 1982, ya fara wa’adinsa na takwas a watan Nuwamba bayan ya lashe zaɓen da aka samu takaddama a kansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng