Layi Ya Zo kan Talakawa, Gwamna zai Raba Naira Biliyan 4 a Mazabun Jiharsa
- Gwamnatin Katsina ta kammala shirye-shiryen raba Naira biliyan 4 ga mazabu 361 domin gudanar da ayyukan ci gaba da al'umma suka zaba
- Kowace mazaba za ta karɓi Naira miliyan 10 bayan amincewar Gwamna Dikko Umaru Radda domin aiwatar da muhimman ayyuka
- Shirin zai ba al'ummomi damar gyara muhimman abubuwan more rayuwa tare da sa ido kan yadda ake aiwatar da kasafin kudin 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina – Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana cewa ta kammala shirye-shiryen raba Naira biliyan 4 ga mazabu 361 na siyasa domin tallafa wa ayyukan gyaran muhimman abubuwan more rayuwa da sauran bukatun ci gaban al'umma.
Mai kula da shirin, Dr Kamaluddeen Kabir, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a gefen taron kare kasafin kudin shekarar 2027 da ma'aikatar kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki ta shirya.

Kara karanta wannan
Wata cuta ta rage mugun iri, ta hallaka ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi jama'a

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa Kabir ya ce ana jiran amincewar gwamna Dikko Umaru Radda ne kawai kafin a fara sakin kudaden.
Yadda za a raba kudin
Kabir ya bayyana cewa kowace daga cikin mazabu 361 za ta karɓi Naira miliyan 10 domin aiwatar da ayyukan da mazauna yankin suka tantance a matsayin mafi muhimmanci.
Ya ce:
"Muna jiran amincewar mai girma gwamna ne kawai kafin mu fara raba kudaden. Kowace mazaba za ta samu Naira miliyan 10 domin aiwatar da ayyukan da al'umma suka zaba."
Ya kara da cewa an tsara shirin ne domin bai wa al'ummomi damar magance matsalolin abubuwan more rayuwa, musamman gyaran gine-ginen gwamnati da suka lalace.
Gwamnati ta gargadi al'ummomi
Kabir ya tuna cewa gwamnatin Katsina ta raba Naira biliyan 5 a karkashin wannan shiri a bara, sannan an sake ware wani Naira biliyan 5 a cikin kasafin kudin shekarar 2027 domin ci gaba da aiwatar da shi.
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar da kananan hukumomi 34 ne ke hada hannu wajen samar da kudi, tare da ba da karin tallafi ga al'ummomin da suka yi amfani da kudaden da aka ba su cikin gaskiya da nagarta.
Sai dai ya gargadi shugabannin al'umma da su tabbatar an yi amfani da kudin yadda ya kamata:
"Ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wata al'umma da aka samu ta karkatar da kudin daga manufar da aka ware su."

Source: Original
Haka kuma ya bukaci al'ummomi su rika bibiyar ayyukan da aka saka a kasafin kudin 2027 domin tabbatar da cewa ma'aikatu da hukumomin gwamnati sun aiwatar da su.
An farmaki alkali a Katsina
A wani labarin, mun ruwaito cewa wani alkalin kotun Shari'a da ke garin Gwarjo a karamar hukumar Matazu ta jihar Katsina ya tsallake yunkurin sace shi bayan wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai hari kotun yayin zaman shari'a.
Rahotanni sun bayyana cewa alkalin, Mohammed Mukhtar, ya tsere ta taga da ke bayan kotun kafin maharan su shiga harabar kotun.
Lamarin ya jefa ma'aikatan kotu, masu kara da sauran mutanen da ke wurin cikin firgici, yayin da maharan suka rika harbe-harbe tare da neman inda alkalin yake.
Asali: Legit.ng
