EFCC na Bincikar Wasu Malaman Musulunci da Limamai kan Laifin Kudi a Najeriya
- Shugaban hukumar EFCC ya tabbatar da cewa suna binciken wasu malamai, fastoci da sauran shugabannin addini kan laifukan kuɗi
- Olanipekun Olukoyede ya ce wasu daga cikin waɗanda ake zargi an riga an same su da laifi kuma suna gidan yari
- Ya yi kira ga shugabannin addini su nuna gaskiya da riƙon amana ta hanyar ayyukansu domin kaucewa fadawa komar hukuma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaban Hukumar Yaƙi da Marasa Gaskiya a Harkokin Kudi ta Najeriya (EFCC), Olanipekun Olukoyede, ya tabbatar da cewa sun bincikar wasu malaman addini kan laifuffukan kudi.
Ya nuna damuwa kan yawan mutanen da ke riƙe da muƙaman addini, kamar malaman musulunci da limaman coci da ake bincike ko gurfanar da su kan laifuffukan da suka shafi harkokin kuɗi a Najeriya.

Source: Facebook
EFCC na bincikar malaman addini
Olukoyede ya ce kundin bayanan shari’o’in hukumar na ɗauke da shari’o’i da dama da suka shafi mutanen da ake kira fastoci, malaman musulmai da sauran shugabannin addini, kamar yadda Tribune ta rahoto.
Ya kuma tabbatar da cewa wasu daga cikinsu an riga aka same su da laifi kuma an hanke musu hukunci, wanda ya sa yanzu haka susna zaman gidan yari.
Shugaban EFCC ya bayyana hakan ne a taron Majalisar Ƙasa na hadin gwiwar addinai (NIREC) karo na biyu na 2026, wanda aka gudanar a Abuja.
Shugaban EFCC ya ba da shawara
Ya ce lamarin ya sa ya fara tambayar ko ya dace a ci gaba da amfani da muƙaman addini a matsayin kariya ko hanyar bayyana matsayin mutum yayin da ake zarginsa da aikata laifi.
“Na ba da shawarar a sake duba muƙaman da muke bai wa mutane a addini. Wataƙila idan zai yiwu mu cire muƙaman nan, fasto da liman. Kun san dalili? Kundin shari’o’ina cike yake da irin waɗannan mutane,” inji Olukoyede.
A cewarsa, kundin shari’o’in EFCC na ɗauke da misalan “fasto kaza” da “liman kaza” da ake zargi da aikata laifukan kuɗi, inda wasu daga cikinsu aka same su da laifi kuma aka tura su gidan yari.
Abin da ya taba faruwa da shugaban EFCC
Shugaban EFCC ya kawo misalin wani mutum da aka kawo hukumar domin bincike, inda ya ce wanda ake zargin ya gabatar da kansa da wasu muƙaman addini bayan an ba shi damar ganawa da shi.
“‘Ni Rabaran ne...’ wanda ake zargin ya gaya masa. Sai na ce, ‘Tsaya a nan, kada ka kawo wannan a nan. Shin ka yi almundahana da kuɗi ko ba ka yi ba?’” ya ba da labarin.
A cewar shugaban EFCC, ana zargin mutumin da karkatar da kuɗaɗe, kuma daga baya ya fuskanci tuhume-tuhume guda biyar.
EFCC ta gano sirrin ma'aikatan gwamnati
A wani labarin, kun ji cewa hukumar EFCC ta gano ma'aikatan gwamnati na tura kudin sata zuwa asusun intanet irinsu asusun manhajojin Crypto.
EFCC ta bayyana cewa a halin yanzu, ta maida hankali wajen yin rigakafi, ta yadda za a hana aikata laifi maimakon ta zo tana bincike bayan an yi barna.
Asali: Legit.ng

