Gwamna a Arewa Ya Tsokano Fada, Kwankwaso Ya Yi Masa Raddi Mai Zafi

Gwamna a Arewa Ya Tsokano Fada, Kwankwaso Ya Yi Masa Raddi Mai Zafi

  • Rabiu Kwankwaso ya ce Gwamnan Benue, Hyacinth Alia, na buƙatar ƙarin koyon dabarun tafiyar da gwamnati da kuma sauraron shawarwari
  • Kwankwaso ya bayyana tare wa da dakatar da tawagar Peter Obi a Benue a matsayin abin takaici, yana mai cewa wasu ’yan APC sun nuna rashin jin daɗinsu
  • Tsohon gwamnan Kano ya ce masu neman zama gwamnoni na buƙatar ƙwarewar siyasa, ilimin gudanar da gwamnati da kuma koyon darussa daga kurakuran magabata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon Gwamnan Kano kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na Nigeria Democratic Congress (NDC), Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi magana kan gwamnan Benue.

Sanata Rabiu Kwankwaso ya ce Gwamna Hyacinth Alia, na buƙatar ƙarin ilmi kan yadda ake tafiyar da gwamnati.

Kwankwaso ya soki Gwamna Alia na Benue
Gwamna Hyacinth Alia tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Fr Rev Hyacinth Iormem Alia, Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Untold Stories with Adesuwa, wanda aka wallafa a YouTube ranar Talata, 22 ga watan Satumban 2026.

Kara karanta wannan

An yi wa su Kwankwaso alƙawarin ƙuri'u miliyan 10 a zaben shugaban kasa na 2027

Ya na magana ne kan lamarin da wasu ’yan daba suka tare ayarin motocin Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, yayin da yake ƙoƙarin shiga Jihar Benue.

Kwankwaso ya soki abin da ya faru a Benue

Kwankwaso ya bayyana lamarin a matsayin “abin takaici wanda bai kamata ba”, yana mai cewa wasu daga cikin ’yan jam’iyyar APC ma sun nuna fushinsu kan abin da ya faru.

“Abin da ya faru a Benue abin takaici ne wanda bai kamata ba. Zan iya gaya muku cewa na samu damar magana da mutum ɗaya ko biyu daga ɓangaren APC, kuma sun fusata sosai saboda bai kamata gwamnan ya yi hakan ba,” in ji shi.

‘Gwamnoni kan daina sauraron shawara’

Kwankwaso ya ce lamarin na nuna abin da ya bayyana a matsayin dabi’ar wasu gwamnoni ta daina sauraron shawarwari bayan sun hau kujerar mulki.

Ya ce wasu shugabanni kan fara tunanin cewa sun fi kowa sani da zarar sun shiga gidan gwamnati, lamarin da ke sa su daina neman shawarwari.

Kara karanta wannan

"Ta wata hanya daban"; Kwankwaso ya ce za su dawo da tallafin man fetur

"Matsalar waɗannan gwamnoni gaba ɗaya ita ce, da zarar ka shiga gidan gwamnati, sai ka ɗauka cewa ka kayar da kowa, kuma ba sa neman shawara,” in ji shi.

‘Akume ne ya fito da Alia daga coci’

Kwankwaso ya kuma yi magana kan yadda Gwamna Alia ya shiga siyasa, yana mai tunawa da dangantakarsa da George Akume, Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma tsohon Gwamnan Benue.

Ya ce Akume, wanda ya kasance gwamna a shekarar 1999 tare da shi, kuma suka yi aiki tare a Majalisar Dattawa, shi ne ya fito da Alia daga coci.

“Abokina, ɗan’uwana, wanda shi ma gwamna ne na 1999, kuma muka kasance tare a Majalisar Dattawa, yanzu kuma shi ne SGF. Akume, George Akume, shi ne ya fito da shi daga coci,” in ji Kwankwaso.

Ya ƙara da cewa a lokacin bai san Alia a matsayin ɗan siyasa ba.

“Ba na ganin shi ɗan siyasa ne. Ban taɓa jin sunansa ba,” in ji shi.
Kwankwaso ya soki Gwamna Alia na Benue
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a wajen taro Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Kwankwaso zai iya sulhu da Gwamna Abba

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce a shirye yake ya sasanta da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, idan gwamnan ya nuna bukatar hakan.

Madugun na Kwankwasiyya ya bayyana cewa zai iya yafewa tare da sulhunta da Gwamna Abba idan shi ma yana son hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng