DSS Ta Bankado Shirin 'Yan Ta'adda na Kai Hare Hare Masallatai da Coci
- DSS ta gargadi shugabannin Musulmi da Kirista a Osun kan zargin shirin ’yan ta’adda na kai hare-hare wuraren ibada da tarukan jama’a
- Shugabannin addini sun samu umarnin ɗaukar matakan kariya, ciki har da hana motoci yin fakin kusa da masu ibada da ƙara tsaron masallatai
- DSS ta ce ana zargin ’yan ta’addan na shirin yaɗa rashin tsaro a Kudu maso Yamma domin haifar da fargaba ko hana gudanar da zaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Osun -Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) ta gargadi shugabannin Musulmi da Kirista a jihar Osun kan wani shirin ’yan ta’adda na kai hare-hare wuraren ibada da sauran wuraren taruwar jama’a.
Rahotanni sun ce ana zargin shirin na daga cikin ƙoƙarin kawo cikas ga babban zaɓen 2027, ta hanyar haifar da rashin tsaro da fargaba a tsakanin al’umma.

Source: Twitter
DSS ta gana da shugabannin addini
Jaridar The Punch ta fitar da rahoto ranar Lahadi, 13 ga watan Satumban 2026 cewa DSS ta gudanar da taruka daban-daban da al’ummar Musulmi da kuma Christian Association of Nigeria (CAN) a Osogbo ranar Laraba.
A tarukan, jami’an tsaron sun shawarci shugabannin addini da su ɗauki matakan kariya domin hana yiwuwar hare-hare.
Wannan ya biyo bayan wani rahoton leƙen asiri da ya nuna cewa ana zargin ’yan ta’adda da shirin yaɗa rashin tsaro zuwa kudancin Najeriya, musamman yankin Kudu maso Yamma.
Ana zargin manufar ita ce haifar da tashin hankali da fargaba yayin da ake tunkarar zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Shugaban Musulmin Osun ya tabbatar
Shugaban Ƙungiyar Musulmin Jihar Osun, Alhaji Mustapha Olawuyi, ya tabbatar da cewa an gudanar da taron da DSS.
Olawuyi ya ce rahoton tsaron gaskiya ne, yana mai cewa an ba shugabannin addini shawarwari kan matakan da za su ɗauka domin kare jama’a.
Ya ce DSS ta bayyana wasu matakai na rigakafi da ya kamata a fara aiwatarwa.
“Taron gaskiya ne; an gudanar da shi ranar Laraba a Osogbo. Muna buƙatar yin taka-tsantsan da kuma kasancewa cikin shiri,” in ji Olawuyi.
Ya kuma ce an daɗe ana ƙoƙarin ganin yadda wasu mutane da ake zargin baƙin haure ne za su kutsa cikin Osun.
An gargadi masallatai su ƙara tsaro
A wani saƙon murya da Olawuyi ya aika wa limamai a faɗin jihar, ya ce jami’an DSS sun zo daga Abuja domin yi wa shugabannin addini gargaɗi kan zargin wani shiri da ’yan siyasa da ’yan ta’adda ke yi na kawo cikas ga zaɓen 2027.
A cewarsa, jami’an sun ce suna da bayanan sirri da ke nuna cewa ’yan ta’addan na shirin matsawa zuwa kudancin Najeriya, musamman Kudu maso Yamma, domin haifar da rikici.
An ce manufar na iya kasancewa hana gudanar da zaɓe ko kuma sanya jama’a cikin fargaba har su ƙaurace wa kaɗa ƙuri’a.
DSS ta shawarci shugabannin wuraren ibada da su ƙara taka-tsantsan, musamman lokacin Sallar Juma’a da sauran manyan taruka.
An hana fakin motoci kusa da masu ibada
A cewar Olawuyi, jami’an DSS sun shawarci masallatai da kada su bar wani mutum ya yi fakin mota kusa da wurin da jama’a ke taruwa yayin Sallar Juma’a ko wani taro.
An kuma gargadi shugabannin masallatai da kada su bari wani mutum ya kwana a cikin masallaci ba tare da saninsa ko dalilinsa ba.
Haka kuma, an buƙaci a yi taka-tsantsan da wasu ’yan achaba da makiyaya da ake zargin an yi amfani da su wajen kutsawa cikin al’umma.
DSS ta kuma ba da shawarar a samar da masu gadi na dare a dukkan masallatai domin ƙara tsaron wuraren ibada.

Source: Original
'Yan ta'adda sun kashe manajan banki
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan ta'adda da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun hallaka wani manajan banki a jihar Imo.
Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, 6 ga Satumba, 2026, yayin da manajan bankin ke kai ’ya’yansa da suke karatu a jami’ar.
Asali: Legit.ng


