'Dalilin da Ya Sa Shugaba Tinubu Zai Lallasa 'Yan Adawa a Zaben 2027'
- Tsohon gwamnan jihar Abia, Sanata Orji Kalu, ya ce Shugaba Bola Tinubu ba shi da wata babbar barazana daga 'yan adawa kafin zaɓen 2027
- Sanata Kalu ya ce rashin haɗin kai tsakanin jam'iyyun adawa ya raunana ƙarfinsu wajen fuskantar APC
- Sanatan ya kuma bayyana cewa aikin gwamnatin Tinubu zai sa al'ummar Arewacin Najeriya su mara masa baya a zaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Abia, Sanata Orji Kalu, ya yi magana kan tazarcen Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.
Sanata Kalu ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba shi da wata babbar hamayya a gabansa kafin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Source: Facebook
Kalu, mai wakiltar mazabar Abia ta Arewa a Majalisar Dattawa, ya faɗi haka ne a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels TV da aka gabatar ranar Laraba, 5 ga watan Agustan 2026.
Ya ce jam'iyyun adawa sun yi rauni matuƙa saboda sun gaza haɗuwa a ƙarƙashin tsari guda da kuma tsayar da ɗan takara ɗaya.
Kalu ya ce 'yan adawa sun yi rauni
A cewar Kalu, Shugaba Tinubu ba shi da wani babban abokin hamayya saboda rashin haɗin kai da ke tsakanin jam'iyyun adawa.
"Ba shi da wata hamayya. 'Yan adawa sun yi rauni sosai. Idan ka duba yadda muka gudanar da zaɓen fidda gwani, yawan mambobinmu da kuma abubuwan da Tinubu ya yi a faɗin Najeriya."
"Musamman sababbin hanyoyin da aka gina, za ka fahimci hakan. Da sun haɗa kai, da hakan zai sa mu fara shiga damuwa. Amma yanzu ba su haɗu ba." In ji shi
Ya ce Tinubu bai tallata ayyuka ba
Sanatan ya amince cewa gwamnatin Shugaba Tinubu ba ta yi nasarar isar da saƙon nasarorin da ta samu ga 'yan Najeriya yadda ya kamata ba. Ya ce shugaban ƙasar bai mayar da hankali wajen tallata ayyukan gwamnatinsa ba.
Kalu ya ƙara da cewa Tinubu yana da "maƙiya da dama" a cikin gwamnati da kuma wajen gwamnati waɗanda ke aiki domin kawo cikas ga tafiyar mulkinsa.
Kalu ya yabawa aikin Tinubu
Kalu ya bayyana cewa shugaban ƙasar ya yi aiki mai kyau har zuwa yanzu. A cewarsa, Tinubu ya kai kusan 65% na abin da ake tsammani daga gare shi, kuma nan da watan Satumba ko Oktoba zai iya kaiwa 70%.
Ya kuma yi hasashen cewa al'ummar Arewacin Najeriya za su mara wa Tinubu baya idan lokacin zaɓe ya yi, saboda abin da ya bayyana a matsayin kyakkyawan aikin gwamnatinsa.

Source: Facebook
Rikice-rikicen adawa kafin zaɓen 2027
Kalaman Kalu na zuwa ne a lokacin da ake ci gaba da samun sauye-sauyen siyasa tsakanin jam'iyyun adawa gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
A shekarar 2025, yunƙurin kafa ƙawancen siyasa a ƙarƙashin jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) ya haɗa fitattun 'yan siyasa da suka haɗa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, da tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.
Sai dai rashin jituwa kan tsarin tafiyar da ƙawancen da kuma shugabancinsa ya haifar da sabon rabuwar kai a tsakanin 'yan adawar. Hakan ya sa Peter Obi da Rabiu Kwankwaso suka fice daga jam'iyyar ADC..
Uba Sani ya yi wa Tinubu alkawari
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya nuna goyon bayansa ga tazarcen Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.
Uba Sani ya bauyana cewa bai shakkar cewa Shugaba Tinubu zai samu kaso 95 na kuri'un mutanen Kaduna a zaben 2027.
Asali: Legit.ng


