Luguden Wuta: Sojoji sun halaka manyan shugabannin yan ta'addan ISWAP guda biyu

Luguden Wuta: Sojoji sun halaka manyan shugabannin yan ta'addan ISWAP guda biyu

  • Sojojin haɗin guiwa MNJTF sun samu nasarar halaka shugabannin kungiyar ISWAP guda biyu a wani farmaki a jihar Borno
  • Bayanai sun nuna cewa Sojojin sun yi wa yan ta'addan luguden wuta na mako ɗaya a Abadam jihar Borno da ke yammacin Tafkin Chadi
  • Manyan shugabannin yan ta'addan da suka bakunci lahira sune, Aba-Ibrahim da kuma Bako Gorgore

Borno - Sojojin rundunar haɗin guiwa (MNJTF) sun halaka wasu manyan shugabannin yan ta'adda na kunguyar ISWAP, Bako Gorgore da kuma Aba Ibrahim, a ƙaramar hukumar Abadam, jihar Borno.

Karamar hukumar Abadam ta jihar Borno na ɗaya daga cikin yankin yammaci a Tafkin Chadi, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Rundunar MNJTF da ke aiki a yankin Tafkin Chadin Najeriya ta kunshi dakarun sojijin Najeriya, Kamaru, da Chadi.

Dakarun sojin Najeriya.
Luguden Wuta: Sojoji sun halaka manyan shugabannin yan ta'addan ISWAP guda biyu Hoto: bbc.com
Asali: UGC

A cewar Zagazola Makama, masanin harkokin tsaro a Tafkin Chadi, manyan yan ta'addan sun mutu ne a wani luguden wuta na tsawon mako da bama-baman jirgin sojin sama na rundunar MNJTF.

Kara karanta wannan

Kwankwaso da wasu manyan jiga-jigan APC sun dira filin Malam Aminu Kano

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A watan Mayu, 2021, Aba-Ibrahim da Bako Gorgore suka jagoranci kai farmaki kan tsagin kungiyar Boko Haram da aka fi sani da Jamā’at Ahlis-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihād (JAS).

A wannan farmakin ne suka kashe shugaban Boko Haram, Abubakar Sheƙau, yayin da wasu kwamandojin 17 aka tilasta musu yin mubaya'a ga ISWAP.

Daga nan Aba Ibrahim ya zama shugaban ƙungiyar ISWAP bayan ya karɓi jagoranci daga Abu-Dawud, yayin da Gorgore ya zama mamba a majalisar Shura ta ISWAP.

Bayanan Fasaha sun nuna cewa sai bayan mutuwar Aba-Ibrahim ne sannan ISWAP ta naɗa, Abu Shuwaram, ɗan shekara 45, wanda ya zama shugaba na 5 a ɓangaren ISIS na nahiyar Afirka, (ISWAP).

A wani labarin na daban kuma Dirama a Kano yayin da tawagar Kwankwaso ta dira gidan Shekarau awanni bayan tafiyar Ganduje

Siyasar Kano ta ƙara rikicewa musamman tsakanin gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Ibrahim Shekarau.

Kara karanta wannan

Kwankwasiyya ta samu karuwa, shugaban yakin neman zaben Tinubu ya rungumi NNPP

Bayan ziyarar Ganduje gidan Shekarau don hana shi komawa NNPP, Kwankwaso ya tura tawaga kafin zuwansa gidan Shekarau.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel