Atiku Ya Samu Damar Mika Sammacin Neman Hana Tinubu Takarar 2027

Atiku Ya Samu Damar Mika Sammacin Neman Hana Tinubu Takarar 2027

  • Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin a mika wa Shugaba Bola Tinubu takardar karar da Atiku Abubakar ya shigar kan cancantarsa ta tsayawa takara
  • Kotun ta bayar da wa’adin kwanaki 7 na mika takardar ga Tinubu ta hanyar jam’iyyarsa ta APC, bayan an kasa mika masa takardar kai tsaye
  • Atiku ya zargi Tinubu da gabatar da wata takardar shaidar NYSC da ya ce ta bogi ce ga INEC, kuma ya bukaci kotu ta hana shi shiga zaben shugaban kasa na 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci a mika wa Shugaba Bola Tinubu takardar karar da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya shigar kan cancantarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a 2027.

Kara karanta wannan

Hankalin Dangote ya tashi kan maido tallafin mai, Atiku ya masa bayani dalla dalla

Kotun ta bayar da kwanaki 7 na mika takardar ga Tinubu ta hannun jam’iyyarsa ta APC, yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen sauraron karar.

Atiku Abubakar da Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu a hagu, Atiku Abubakar a hagu. Hoto: Bayo Onanuga|Paul Ibe
Source: Facebook

Kotu ta ba Atiku kwana 7

Vanguard ta wallafa cewa mai shari’a Inyang Ekwo ne ya bayar da umarnin a yi wa Tinubu madadin mika takardar, wato a mika masa ta hannun jam’iyyarsa ta APC.

An bayar da umarnin ne bayan lauyan Atiku, Olanrewaju Omotayo-Ojo, ya gabatar da bukatar a gaban kotu a madadin Silas Onu, wanda aka ce yana zaman makoki.

Shari’ar mai lamba FHC/ABJ/CS/1888/2026 ta shafi Atiku da ADC a matsayin masu kara, yayin da Tinubu, APC da INEC suke cikin wadanda ake kara.

Zargin Atiku ga Bola Tinubu

A cikin rantsuwar da ya gabatar wa kotu mai sakin layi 25, Atiku ya yi zargin cewa Tinubu ya gabatar da wata takardar shaidar kammala NYSC da ba ta dace da sunansa ba ga INEC.

A cewar Atiku, takardar da aka gabatar tana dauke da sunan “Tinubu Bola Adekunle”, yayin da ya ce sunan shugaban shi ne Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Takarar 2027: INEC ta goyi bayan Tinubu a kan Atiku a shari'ar da ake yi a kotu

The Sun ta wallafa cewa Atiku ya bukaci kotu ta yi la’akari da wannan batu wajen tantance cancantar Tinubu na tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027.

Abin da Atiku ke nema a kotu

Atiku ya bukaci kotu ta tabbatar da cewa gabatar da takardar da ya kira ta bogi ga INEC ya saba wa tanadin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.

Ya kuma bukaci kotu ta hana Tinubu da APC shiga zaben shugaban kasa na 2027 bisa zargin gabatar da takardar shaidar NYSC da ba ta inganta ba.

Shugaban jam'iyyar APC
Shugaban APC, Nentawaye Yilwatda. Hoto: All Progressive Congress
Source: Facebook

Sai dai wadannan zarge-zarge ne da Atiku ya gabatar a cikin karar, kuma ba hukuncin kotu da ya tabbatar da cewa takardar bogi ce ba.

A yanzu haka dai kotun ta riga ta sanya ranar 28 ga Satumban 2026 domin fara cikakken sauraron shari’ar.

Maganar a zabi Tinubu a 2027

A wani labarin, kun ji cewa Oba Ewuare II, Sarkin Benin, ya nuna goyon bayansa ga burin Shugaba Bola Tinubu na neman wa’adi na biyu a 2027.

Sarkin ya bayyana hakan ne ranar Talata lokacin da tawagar kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC ta kai ziyara fadarsa domin neman albarkarsa.

Tawagar ta kunshi Darakta-Janar na kwamitin, Abdulaziz Yari, da Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, tsohon Gwamnan Sokoto Aliyu Wamakko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng